Gwamnonin PDP ba sa son a kawo karshen rikicin makiyaya – Buhari.

Date:

Fadar Shugaban Najeriya a ranar Laraba, ta zargi gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP, da kin goyon bayan kudirin kawo karshen rikicin makiyaya a kasar ta yadda za a ceci rayukan jama’a da dukiyoyinsu.

Fadar Shugaban kasar na bayyana hakan ne bayan taron da kungiyar Gwamnonin PDP ta gudanar a karshen mako a Uyo, jihar Akwa Ibom ranar Litinin.

A martaninta fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja, ya ce gwamnonin PDP ba su samar da mafita ga matsalolin kasar ba amma sun fi sha’awar abin da ya shafe su .

A cewar sanarwar: “Wannan shirin na samar da matsuguni ga makiyaya ya kawo ‘yanci da sauyi na zamani don kawo mafita ga kalubalen da al’ummomi daban-daban na kasarmu suka fuskanta amma gwamnonin PDP suka ki amincewa da shi, suka hana dukkan’ yan Najeriya ‘yancinsu na tsarin mulki na rayuwa da aiki a kowace jiha ta Tarayya sun fi son yin kira ga rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yan Najeriya”

86 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...