Daga Sadeeq Ali
Shahararren Malamin Addinin Musulmcin nan Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yayi Tsokacin Kan Marin da Wani ya yiwa Shugaban Kasar Faransa a bainar jama’a.
Sheikh Daurawa a Sahihin shafinsa na Facebook yace Wannna abun daya faru da Shugaban na Faransa aya ce da Allah ya nuna Saboda abin Daya goyi baya aka yiwa Annabi S A W.
“WANI YA MARI SHUGABAN FARANSA A BAINAR JAMA’A”
ALLAHU AKBAR. ALLAH YA ƘARAWA ANNABI, SAW, DARAJA DA FADHILA DA WASEELA DA DARAJATUL RAFEE’ATAH.ان شانئك هو الابتر”LALLAI MAI MUZANTAKA SHINE MAI YANKAKKEN BAYA.”
YA BAYYANA CEWA CIN MUTUNCIN ANNABI YANA DAGA CIKIN YANCIN BAYYANA RA’AYI A DOKOKIN FARANSA,SHI KUMA MARINSA DA AKA YI MA JI, WACCE DOKA CE ZATA ƘARE HAƘƘIN WANDA YA MARE SHI,” Inji Sheikh Daurawa