Aisha Buhari ta Rufe Shafinta na Twitter

Date:

Mai dakin shugaban Najeriya Aisha Buhari ta rufe shafinta na Twitter jim kadan bayan sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta dakatar da shafin a Najeriya a yammacin ranar Juma’a.

“Zan rufe shafina na Twitter a yanzu. Fatan alheri ga Najeriya,” kamar yadda ta rubuta gabanin rufe shafin.

Zuwa safiyar ranar Asabar mafi yawan masu amfani da shafin na Twitter ba sa samun damar shiga, sai dai ta wata manhajar intanet mai suna VPN.

Dan haka ko sun sanya wani abu a shafin nasu zai zama ya fita da sunan wata kasar daban ba Najeriya ba.

Tun da farko sai da Ministan yada labaran kasar Lai Mohammed ya yi zargin kamfanin Twitter baya tafiyar da abubuwansa bisa gaskiya a Najeriya, ya kara da cewa shi yasa gwamnati ta yanke hukunci ta dakatar da shi.

Wannan dai duka na zuwa ne kwana biyu bayan da Twitter ya goge wani bayani da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi, wanda yake gani ya saba ka’idojinsa.

282 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...