Jamia’ar Wudil za ta hukunta mazan da suka yi wa ɗaliba ihun saka abaya

Date:

Mahukuntan jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil dake nan Kano ta ce za ta ɗauki “mummunan mataki” kan ɗaliban da suka ci zarafin wata ɗaliba saboda ta saka rigar abaya.

Cikin wata sanarwa da makarantar ta fitar a jiya Talata, shugaban sashen harkokin ɗalibai ya nemi afuwar ɗalibar sannan ya buƙaci ta shigar da ƙara a hukumance domin neman haƙƙinta.

A jiya Talata ne aka ga wasu matasa na jan abaya da wata ɗaliba ta saka tare da yi mata ihu cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta a wani wuri da aka ce cikin jami’ar ne ta Wudil.

“Hukumar Kano University of Science and Technology Wudil ta samu ƙorafe-ƙorafe daga shafukan zumunta game da wata ɗaliba da ɗalibai maza suka ci zarafinta saboda ta saka abaya,” a cewar sanarwar.

“Ni shugaban sashen harkokin ɗalibai zan ɗauki mummunan mataki a kan wannan lamari. Ɗalibai su sani cewa su ba hukuma ba ce da za su ci zarafi ko ɗaukar mataki kan wani, sai dai kawai su kai rahoto wurin jami’an tsaro.”

Sanarwar ta ce abaya ba ta saɓa wa dokar saka tufafi ta jami’ar ba, “saboda haka ɗalibar ba ta karya wata doka ba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba gaskiya a bayanin wasu Manoman Kano da suka ce Muna karbar kudi a wajensu – Civil defense

Rundunar tsaro ta Civil defense ta Kasa reshen jihar...

Korar ma’aikata a Kano: Bashir Gentile ya yiwa Faizu Alfindiki martani mai zafi

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Masanin kimiyar siyasa kuma mai sharhi...

Sakataren kungiyar NRO Abdulkadir Gude ya rasu

Allah ya yi wa dattijo, kuma Sakataren kungiyar Northern...

Gwamnatin da ta ke korar Ma’aikata ba ta Cancanci Wa’adi na biyu ba – Faizu Alfindiki

Daga  Maryam Muhammad Ibrahim   Abin takaici ne ganin yadda gwamnatin...