2023: Abba Gida-Gida ba shi bane Dan takarar Gwamna – Kwankwaso

Date:

Daga Halima A Musa

Abba Gida-Gida ba shi bane Dan takarar  a 2023 – Kwankwaso
 Tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso na duba yiwuwar tsige Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamna a tutar jam’iyyar PDP a Shekara ta 2023.


 Ya ce jam’iyyar da tafiyar Kwankwasiyya ba su yanke hukunci ba kan wanda ya kamata a tsayar a Shekarar 2023.


 Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da tsagin Dr Yunusa Adamu Dangwani da sauran masu ruwa da tsaki sakamakon rikicin cikin gida da ke kawo cikas ga harkar a makwannin da suka gabata.


 Politics Digest ta rawaito cewa rabon kayan Azumi a watan Ramalana da Dr Yunusa Adamu Dangwani ya yi ya haifar da baraka a tafiyar Kwankwasiyya inda wasu mambobin da ke goyon bayan takarar Abba Kabir Yusuf suka zarge shi da yi wa Kwankwaso zagon kasa.


 A wani faifan bidiyo da sakataren tsare-tsare na PDP Sanusi Surajo Kwankwaso ya zargi Dangwani da kokarin wargaza kungiyar saboda kinsa ga Takarar Abba Kabir Yusuf a zaben 2019.


Kadaura24 ta rawaito A cikin martanin da ya yi, yayin ganawa da manema labarai, Dangwani ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa zai fito takarar gwamna yana mai bayyana cewa lokaci bai yi ba .


 A wata ganawa da ya yi a daren Litinin din data gabata wadda ta dauki tsawon awanni uku a gidansa da ke miller road a kano, Kwankwaso ya tabbatar wa masu ruwa da tsakin cewa jam’iyyar ba ta da dan takarar gwamna gabanin shekarar 2023 yana mai cewa lokaci bai yi ba, jam’iyyar za ta fitar da dan takararta ta hanyar dimokiradiyya.


 A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunan ta, tace wasu masu ruwa da tsaki Daga tsagin Dangwani sun gabatar da kokensu Kan yadda bangaren Abba Kabir suke nuna musu yatsa da Kuma rashin girmama jagoransu Inda Suka bukaci su rika girmama su a matsayinsu na masu ruwa da tsaki a tafiyar Kwankwasiyya.


 Majiyar ta ci gaba da bayyana cewa Kwankwaso ya yi taka-tsan-tsan a wannan karon, yana kokarin kwantar da hankalinsu domin sasanta lamarin duba da batutuwansa tare da shugabancin jam’iyyar PDP na kasa da kuma rikice-rikicen taron shiyya da aka yi a Kaduna.


 “Oga ba shi da kyakkyawar alaka da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar mu a shiyyar Arewa maso Yamma, jam’iyyar a matakin kasa ba ta ji dadin yadda yafi fifita Kwankwasiyya akan jam’iyyar ,kuma idan ya bar rikicin cikin gida na Kwankwasiyya ya kara ta’azzara a Kano to labarin zai zama daban.”Inji Majiyar tamu


 Don haka, ya yi taka tsan-tsan a wannan karon kuma masu ruwa da tsaki suna da iko sosai, suna da dimbin magoya baya a harkar ba kamar Abba ba wanda ba ya tare da mutane lokacin da yake Kwamishina ba.

 Wadanda suka halarci taron sun hada da Barista Maliki Kuliya, tsohon babban lauyan jihar Kano, Yusuf Bello Dambatta, Garba Ibrahim Diso, Yunusa Adamu Dangwani, Lawan Sale Gaya, Zainab Audu Bako da dai sauransu.


 A Yayin taron mambobin kungiyar  wanda ya gudana a ranar Talata a Miller Road, Kwankwaso ya tabbatar wa da kowa cewa babu wani dan takarar gwamna ko wani mai son tsayawa takara a cikin tafiyar inda ya bayyana cewa halin da ake ciki ya kamata kowa ya kiyaye

289 COMMENTS

  1. Смотреть онлайн прямую трансляцию боя Энтони Джошуа – Александр Усик 25.09.2021 Бокс Видео бокса AnthonyJoshua Олександр Усик Ентоні Джошуа

  2. Усик: Не могу сказать, что Джошуа меня впечатлил – СПОРТ OleksandrUsyk Що відомо про бій Усик — Джошуа. Дату бою призначено на суботу, 25 вересня. Він відбуватиметься у Лондоні, а битимуться боксери за володіння титулами чемпіону світу в суперважкій вазі IBF, WBO

  3. Усик – Джошуа: 7 речей, які об’єднують боксерів. Непросте дитинство загартувало спортсменів, які забезпечили безбідне життя своїм матерям Александр Усик Энтони Джошуа смотреть онлайн Усик проти Джошуа. Чого чекати від поєдинку Сюжет Корреспондент.net, 14 вересня 2021, 19:51

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...