Yajin Aiki:El-Rufai ya kori dukkanin ma’aikatan jinya na jihar Kaduna

Date:

Gwamnatin Kaduna ta sanar da korar dukkanin ma’aikatan jinya da ba su kai matakin aiki 14 ba.

Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai, ta sanar sake korar ma’aikatan ne a ranar Talata duk da boren da ta ke fuskanta na neman dawo da dubban ma’aikatan da aka kora.

Matakin gwamnan na korar ma’aikatan jinyar yana da nasaba da wani labarin da ya wallafa a Twitter da ke zargin ma’aikatan da katse iskar oxygen daga wani jariri a asibitin koyarwa na Barau Dikko a ranar Litinin da ƙungiyar ƙwadago ta kira yajin aiki.

Sanarwar da gwamnatin Kaduna ta fitar ta ce “baya ga gabatar da buƙatar neman a hukunta ma’aikatan ga ma’aikatar shari’a, gwamnati kuma ta sanar da korar dukkanin ma’aikatan jinya da ba su kai matakin aiki na 14 ba saboda yajin aikin da suka shiga ba bisa ka’ida ba.”

“An ba ma’aikatar lafiya umurnin ta tallata neman aikin sabbin ma’aikatan jinya cikin gaggawa domin maye gurbin waɗanda aka kora sannan albashinsu za a ba ma’aikatan da suka ci gaba da aiki a matsayin kuɗaɗen lada,” in ji sanarwar.

Sannan kuma gwamnatin ta ba dukkanin ma’aikatun jihar umurnin gabatar da rijistar ma’aikatan da ke zuwa aiki ga sakataren gwamnati da kuma kwamishinan ilimi.

140 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...