Jam’iyyar APC tace ta yiwa Mutane Miliyan 40 Rijistar Jam’iyyar a Nigeria

Date:

Jam’iyyar A P C ta ce yawan membobinta a fadin kasar ya haura miliyan arba’in.


 Sakataren, Kwamitin riko na kasa na jam’iyyar, Sanata John Akpanudoedehe ya bayyana haka lokacin da shugaban kwamitin rikon jam’iyyar na kasa kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya karbi bakuncin wasu jakadun jam’iyyar a Abuja.


 Sanata Akpanudoedehe ya ce kafin kwamitin ya fara rajistar membobin jam’iyyar da aka kammala, membobinsu basu wuce sun mutane miliyan 12.


 Ya ce Kwamitin na rikon kwarya ya iya dawo da Yan jam’iyyar da aka rasa kuma ya sami sababbi a cikin gwamnatin APC, ci gaban da ya jaddada yana da kyau ga jam’iyyar.


 Tun da farko, Shugaban riko, Mai Mala Buni, ya bukaci sabbin jakadun da su da su yiwa kasar nan kyakkyawan aiki a duk inda aka tura su.


 Jagoran tawagar kuma babban kwamishina a Zambiya, Ambasada Nwanne Ominyi, ta bayyana shirye-shiryensu na sauke nauyin da ke kansu na kasa da jam’iyyar kamar yadda ta shirya wa 2023

245 COMMENTS

  1. Усик Джошуа — дивитися онлайн бокс — пряма трансляція бою Смотреть онлайн прямую трансляцию боя Энтони Джошуа – Александр Усик 25.09.2021 Бокс Видео бокса Думаю, що природні габарити Джошуа, його сила, швидкість, молодість і навички можуть зробити вечір дуже важким для Усика, особливо на початку бою.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Korar ma’aikata a Kano: Bashir Gentile ya yiwa Faizu Alfindiki martani mai zafi

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Masanin kimiyar siyasa kuma mai sharhi...

Sakataren kungiyar NRO Abdulkadir Gude ya rasu

Allah ya yi wa dattijo, kuma Sakataren kungiyar Northern...

Gwamnatin da ta ke korar Ma’aikata ba ta Cancanci Wa’adi na biyu ba – Faizu Alfindiki

Daga  Maryam Muhammad Ibrahim   Abin takaici ne ganin yadda gwamnatin...

Zaizayar kasa: Gwamna Abba gida-gida ya raba diyyar Naira Miliyan 600 A Kano

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...