Ganduje Ya Yiwa Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Ta’aziyar Rasuwar Mahaifiyarsa

Date:

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa

Gwamnan jihar Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje ya jajantawa gwamnan farar hula na farko na jihar Jigawa, Alhaji Ali Sa’ad Birnin Kudu bisa rasuwar mahaifiyarsa Hajiya Hafsat Sa’ad Birnin Kudu wacce ta rasu kwanan nan bayan fama da rashin lafiya.

Marigayi Hajiya Hafsat Sa’ad Birnin Kudu Mai shekaru 83 ta rasu ta bar ‘ya’ya 7 da jikoki 63.

A cikin sakon nasa, Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa Dr.Nasiru Yusuf Gawuna a wajen jana’izar marigayiyar wanda ya gudana a Masallacin Umar Ibn Khattab ya mika ta’aziyar sa ga iyalai, gwamnati da jama’ar Jihar Jigawa.

“Allah Ya ba ku da kuma dukkan danginku karfi da kuma kwarin gwiwa don jure wannan rashi da ba za a iya mantawa da shi ba. Gwamnati da jama’ar jihar Kano suma suna cikin alhinin rasuwar Hajiya Hafsat”.

Cikin sanarwar da Babban Sakataren yada labaran Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Hassan Musa fagge ya sanyawa hannu Kuma ya aikowa Kadaura24 yace yayin da yake addu’ar Allah ya jikan marigayiya Hajiya Hafsat Sa’ad Birnin Kudu yana Yi fatan Allah ya ba ta Jannatul Firdaus.

128 COMMENTS

  1. Бій Ентоні Джошуа проти Олександра Усика (англ. Anthony Joshua vs. Oleksandr Usyk) — майбутній професійний боксерський поєдинок, який відбудеться між чемпіонами WBA (Супер), IBF, WBO та IBO у важкій вазі Ентоні Джошуа та колишнім Джошуа Усик смотреть онлайн Усик – Джошуа: смотреть онлайн-трансляцию боя 25.09.2021. Украинский супертяжеловес Александр Усик (18-0, 13 КО) проведет поединок против британского чемпиона wba, wbo и ibf Энтони Джошуа (24-1, 22 КО).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...