Rashin Mai Babban Daki Zai bar gibi Mai yawa a Kano – Alhassan Ado Doguwa

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai ta Kasa Kuma Dan Majalisa Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Tudun Wada da Doguwa Hon. Alhassan Ado Doguwa ya aike da sakon ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyar Masu Martaba Sarakunan Kano da Bichi ga iyalanta da al’ummar jihar Kano baki Daya.

Cikin Wata sanarwa Mai dauke da sa hannun Mataimaki na musamman ga Shugaban Majalisar Wakilai Auwal Ali Sufi utai ya aikowa Kadaura24 ya bayyana Rasuwar Hajiya Maryam Ado Bayero a Matsayin babban Rashi ba ga ga iyalanta kadai ba har da al’ummar jihar Kano Dana Kasa baki daya.

Alhassan Ado Doguwa yace Marigayiyar Mace ce Mai kyakykyawan Halaye Kuma uwa ce abar koyi saboda irin Tarbiyyar data baiwa ‘ya’yanta lokacin tana Raye.

“Salon yadda Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Dan uwansa Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero suke mulkar al’ummarsu ya nuna Hajiya Maryam Ado Bayero (Mai Babban Daki ) ta basu Tarbiyya ta Gari”. Inji Alhassan Ado Doguwa

Shugaban Masu Rinjayen yayi Mata addu’ar samun Rahamar Allah madaukakin Sarki tare d fatan Allah ya baiwa Iyalan da al’ummar jihar nan hakurin jire Wannan babban Rashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Za a sanya Maiwushirya da Ƴar Guda cikin shirin auren gata – Hisbah

  Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yaba da hukuncin...

RMK@69: Tinubu ya yi wa Kwankwaso kyakykyawan yabo

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika sakon taya...

NAHCON ta kafa kwamitin sa ido kan harkokin jiragen sama domin aikin Hajjin 2026

Shugaban Hukumar Kula da Alhazai ta Kasa (NAHCON), Farfesa...

An Fara Binciken Wani Tsohon Gwamna Kan Zargin Daukar Nauyin Yiwa Tinubu Juyin Mulki

Rahotanni sun bayyana cewa ana binciken wani tsohon gwamna...