BUDADDIYAR WASIKA ZUWAGA MAIGIRMA COMMISSIONER NA MA’AIKATAR ILIMI TA JAHAR KANO.

Date:

HALIN DA MAKARANTAR MATA SECONDARY TA BABBAR MAZABAR BEBEJI LG KE CIKI AYAU.

Wannan makaranta takasance makarantar da take da yawan dalibai wanda akalla akwai yara daga kusan mazabu Hudu dakuma kauyuka akalla bakwai dasuke zuwa wannan makaranta domin daukar ilimi. Tare da kasancewar kuma ita kadaice makarantar mata a wannan yanki, babu koda kuwa private school wacce akallazata rage population.
Saidai kash wannan makaranta tana cikin wani hali dangane da tashin permanent site, babu koda rabin classes dazasu dauke adadin wannan dalibai.
GGASS BEBEJI tanada kwata kwata ajujuwa guda shida (6 classes) wanda kowanne daya daga ciki baya daukar koda rabin adadin dalibanda ake dasu na wannan particular aji.
Akwai dalibai akalla 2,000+ a wannan makaranta, Hakika hakan yana matukar sarewa malaman wannan makaranta gwiwa akan classroom control da management.

Babban masallacin jumaa na Bebeji shine wurin da ake samu a saka wasu daga cikin daliban, Saigashi yau kwatsam an wayi gari Liman da Na’ibinsa dakuma ‘yan tawagassa sun koro yaranmu waje kamar dabbobi sunce baza’a kara karatu aciki ba.

Akarshe, Amatsayina na shugaban Kungiyar dalibai ta mazabar Bebeji BESU ina kira ga megirma kwamishinan Ilimi Sanusi Muhammad dakuma sauran mahukunta na garin Bebeji da masu Kudin garin Bebeji dasu shigo wannan lamarin su kawowa makaranta dauki.

THE PRESIDENT
BEBEJI STUDENTS UNION (BESU)
IBRAHIM DANJUMA ZUBAIRU BEBEJI

16 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...