Hana Twitter: Za mu hadu a kotu da NBC, inji Masu AIT,Raypower

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Suleman


 Kamfanin DAAR Communications PLC, masu  gidajen Talabijin na AIT da Raypower FM da Faaji Radio, sun ce za su garzaya kotu domin kalubalantar matakin da Hukumar Kula da Kafafen yada Labarai ta Kasa ta dauka kan dakatar da Twitter da Gwamnatin Tarayya ta  sanar da cewa da zarar an kammala yajin aikin da Ma’aikatan Shari’a suke yi aTarayyar Najeriya.


 Sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Litinin, Mai dauke da sa hannun shugabannin kamfanin.


 Sanarwar ta ce haramta Twitter da Gwamnatin Tarayya tayi baya Cikin wata doka ta yada labarai a Kasar Nan, don Haka Suna ganin Matakin Bai dace ba.


 AIT, Raypower da Faaji Radio sun dakatar da amfani da shafin su na Twitter amma zasu kalubalanci umarnin NBC a kotu da zarar ma’aikatan shari’a sun dakatar da yajin aikin da suke yi.


 Idan za’a iya tunawa NBC, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ta umarci dukkan tashoshin watsa labarai a duk fadin kasar nan da su dakatar da ayyukan su na Twitter tare da daina amfani da shi a matsayin kafar watsa labarai ko kafar Samun labarai.  Umurnin ya kuma bukaci su Dakatar ayyukansu a shafin microblogging.


 Wannan ya biyo bayan dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya da Gwamnatin Tarayya ta yi game da amfani da dandalin don ‘ayyukan da za su iya lalata kasancewar kamfanin na Najeriya.


 NBC ta nakalto daga Sashe na 2 (1), 3.11.2 da kuma 5.6.3 na dokar NBC , Inda tace da Wadannan Sassa Hukumar tayi wukar kugu wajen Dakatar da aiyukan Kafafen yada labaran a Twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...