Gyaran Makarantu: Ganduje ya rabawa K/H Naira Miliyan 800

Date:

Daga Nazir Hamza Muhd

Gwamnatin jihar Kano tace zata Kara Kashe Naira Miliyan 800 a karo na biyu domin gyarawa da Gina sabbin ajujuwa da Kuma Bandakuna a Wasu Daga Cikin Makarantun Firamare dake Kananan Hukumomi 44 na jihar nan.

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan Yayin daya jagoraunci karbar rahoton yadda aka Kashe Naira Miliyan 880 ga kowacce Karamar Hukuma wajen gyaran azuzuwa a Watannin baya da suka gabata.

Gwamna Ganduje yace gwamnatinsa ta Maida hankali sosai ga fannin ilimi domin sai da Ilimi ake samun al’ummar da zata iya amfanar da kanta kuma ta amfani da Wasu.

“Mun dauki Ilimi da muhimmanci gaske shi yasa muka Mai da Ilimin ya Zama kyauta Kuma dole , Saboda mu bada Dama ga ‘ya’yanmu su Sami Ilimi, Kuma bayan aiyana Wannan kudiri namu Muna bada isassun kudade domin ganin ba’a Sami tasgaru ba wajen baiwa yaran Ingantaccen Ilimi”. Inji Ganduje

Yace a baya gwamnati ta kashe Naira Miliyan 880 wajen ginawa da gyara azuzuwa a Kananan Hukumomi Kuna Tuni aka Kammala aiyukan Kuma gwamnan yace ya gamsu da yadda aka gudanar da aiyukan.

Ganduje yace a Wannan karonma gwamnatin zata Kashe Wadancan kudade domin Kara ingantawa da Samar da kyakykyawan yanayin koyo da koyarwa da Kuma Kara tabbatar da Kudirin gwamnati na Samar da way Ilimi kyauta ga al’ummar jihar Kano.

Yayin da yake nasa jawabin Shugabanin Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano Dr Danlami Hayyo yace Daga Shekara ta 2015 zuwa Wannan Shekara gwamnatin Jihar Kano ta Gina azuzuwa guda 1,396 .

Dr. Hayyo yace gwamnati na iya bakin kokarin ta wajan inganta harkokin Ilimi tun Daga tushe a jihar Kano,duba da yadda take bada nata kaso akan lokaci ga Hukumar Ilimin Bai Daya ta Kasa domin samun damar karbar tallafin da Hukumar take baiwa jihohi domin bunkasa harkokin Ilimi a jihar.

Kadaura24 ta rawaito cewa Yayin taro an Mika takardun shaidawa Fara sabbin aiyukan ga Yan kwangila da Kuma baiwa Nakasassu tallafin kayan karatu irin wadanda suke bukatar don bunkasa Ilimin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...