Mun himmatu wajen tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana – Muhd Abba Danbatta

Date:

Daga Sayyadi Abubakar Gwagwarwa
 Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta jaddada kudirinta na ganin an gudanar da aikin Hajjin bana cikin nasara.
 Sakataren zartarwa na hukumar Alhaji Mohammad Abba Danbatta ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
 Ya ce bayan dage haramcin da gwamnatin Saudiyya ta yi wa wasu kasashe ciki har da Najeriya na shiga cikin kasar, shirye-shirye na cigaba da kankama wajen gudanar da aikin Hajji cikin nasara.
 Sakataren zartarwa ya bayyana cewa hukumar za ta yi la’akari da wadanda suka ajiye kudin aikin hajjin su a hukumar a Shekaru biyu da Suka gabata gabanin na Masu biya yanzu.
 “Wadanda suka ajiye kudadensu a hukumar za a fara tantance su, kuma ina tabbatar muku duk za su samu kujeru muddin sun kammala biyan kudin su”.Inji Muhd Abba
 Alhaji Mohammad Abba Danbatta ya Kara da cewa hukumar ba ta fara karbar kudaden ajiyar kudin aikin hajji ba, yana mai cewa hukumar na jiran Hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON ta raba kujerun ta baiwa Jihar Kano na ta.
 Ya bayyana cewa hukumar za ta fara bitar maniyatan a watan Ramadan da kuma bayansa, Inda yace bayan azumi Ramadan zata Dora da bitar kullum-kullum domin samun nasarar gudanar da ayyukan Hajjin na bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...

Kamata ya yi wajen Mauludi ya Zama waje Mai nutsuwa saboda ana ambaton Allah da Manzonsa – Mal Ibrahim Khalil

Shugaban Majalisar shuhurar Malamai ta jihar Kano Sheikh Malam...

Ra’ayi:‎Tsarin Kwankwasiyya ya dora Kano a gwadaben cigaba a mulkin Gwamna Abba Kabir -Adamu Shehu Bello

‎ ‎Ra’ayi ‎ ‎Daga Adamu Shehu Bello (Bayero Chedi), Jigo a Kwankwasiyya...