Daga Sadiya Muhd Sabo
Babban Darakta na rukunin Dangote kuma shugaban kungiyar masana’antu ta Najeriya (MAN) Engr. Mansur Ahmed ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa matatar man dangote da ake yi za ta taimaka wajen shawo kan matsalar karancin man fetur a kasar nan.
Kadaura24 ta rawaito wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai na jihar Kaduna da kuma ministan tsaro Bashir Salihi Magashi suke yabawa Kamfanin na Dangote.
Rukunin Kamfanin Dangote na daya daga cikin wadanda suka yi nasara a kasuwar baje kolin da aka kammala ranar Lahadi a Jihar kaduna.
Mansur Ahmed ya kuma ce matatar man da za ta fara aiki nan da shekara mai zuwa za ta yi tasiri sosai ga tattalin arzikin Najeriya, domin zai taimaka wajen adana kudaden waje da kuma samar da ayyukan yi ga al’umma.
Ya bayyana wannan tasiri mai kyau a matsayin babban abin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Najeriya.
Ahmad wanda yayi jawabi a karshen mako a wurin bikin ranabta musamman na Dangote a bikin baje kolin kasuwancin kasa da kasa na Kaduna karo na 43 da aka gudanar, ya ce shugaban rukunin Dangote Alhaji Aliko Dangote yana da kishi da kuma burin sauya yanayin tattalin arzikin Afirka ta hanyar bunkasa masana’antu.
Babban daraktan rukunin ya kuma Kaddamar da takin Dangote a hukumance ga yan kasuwa a Kaduna da jama’a, inda ya bayyana farin cikinsa kan yadda sabon samfurin zai taimaka wajen magance matsalolin da ake fuskanta a harkokin noma.
Ya yabawa Cibiyar Kasuwanci masana’antu ma’adanai da harkokin noma‘yan kasuwan ta Jihar kaduna (KACCIMA) Waɗanda su ne suka shirya taron baje kolin har aka sami nasara.
Da yake jawabi, Shugaban KADCCIMA Alhaji Suleiman Aliyu ya bayyana hadin gwiwa da Kamfanin Dangote a matsayin mai matukar muhimmanci dake bunkasa harkokin kasuwanci a kasar nan.
Ya ce ba za a iya kididdige irin goyon bayan da rukunin Dangote ke ba don samun nasarar wannan baje kolin.
Babban Manajan Rukunonin Kamfanin Bello Dan-Musa ya ce kamfanin ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen bunkasa tattalin arzikin kasa zagon kasa, sai dai ta hanyar ayyukan jin kai da dama, wanda tsare-tsarensa na Corporate Social Responsibility da Gidauniyar Aliko Dangote suka wakilta.
Wakilan Rukunonin Kamfanin Dangote su ma sun yi jawabi kan kayayyakin da kamfanin ya samar. Su ne: Alhaji Abdulsalam Waya (Dangote Sugar), Alhaji Ahmed Tijana (Dangote Siminti), Mista Isaac Oladele (Takin Dangote ) da Mista Ifeanyi Tobi (Gishirin Dangote).