Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin mafi lalacewa cikin jam’iyyun siyasa a wannan lokaci, dukda dai yace itama PDP ba kanwar lasa bace wajen kama-karya a yanzu, domin duk cancantarka da haƙƙin ka, zaka iya rasa shi ta dalilin wasu sojojin gona.
Kadaura24 ta rawaito cewa, Kwankwaso ya bayyana haka ne jiya Lahadi, yayin taron masu ruwa da tsaki na Kwankwasiyya a gidansa dake Kano, inda yace har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, amma shirye-shirye sunyi nisa a tsakaninsa da jam’iyyar NNPP mai kayan marmari.
Kwankwaso yace fita daga jam’iyya da komawa ba illa bane, kuma hakan ma shi ne kwarewa a siyasa, domin a shekarar 2018 da sukayi zaben fidda gwani a Fatakwal, wadanda suka zo na farko, na biyu, na uku dana hudu, duk sunbar PDP sun dawo, sai kuma wasu tarkace da suka biyo baya, a cewar Kwankwaso.