Sabuwar Makarantar da Gidauniyar Alfajr gina a Kano za ta Magance Matsalar barace-barace – Sheikh Elmulla

Date:

Daga Umar Hussain Mai Hula

 

Gidauniyar alfajr ta kaddamar da wata sabuwar makaranta Mai suna Alfajr college of education wadda aka Samar da ita domin koyar da Ɗalibai karatu kyauta tun daga farawa har Zuwa Lokacin kammala Makarantar.

Yayin da yake ganawa da wakilin Kadaura24 Jagoran Makarantar  Sheikh Abdulkhaliq Elmulla yace an samar da Makaranta ne domin Inganta harkokin addinin Musulunci Musamman Karatun Karatun alqur’ani Mai girma.

Sheikh Abdulkhaliq Elmulla yace Makaranta ta zo da tsarin bada Ilimin alqur’ani kyauta ga Kananan Yara Musamman a tsarinsu na haddace alqur’ani da ka’idojin da Cikin Shekara Guda, Wanda akai Masa Suna (Tajur Wakar).

Yace an samar da Wannan tsari ne da nufin rage kukan da Gwamnati take yi akan yawan Samun Yara mabarata a akan titi, yace idan iyayen Yara Suka gane Shirin zasu daina tura ‘ya’yan su almajiranci.

Sheikh Elmulla ya Kara da cewa akwai tsarin gyarawa mahaddata alqur’ani karatunsu ta hanyar koyawa musu dukkanin wasu ka’idojin alqur’ani da Kuma kira’o’in Guda goma da tafsiri da dai Sauransu Kuma yace shi ma Wannan tsari kyauta ne.

” Muna iya daukar Waɗanda suka iya karanta alqur’ani Karatu kubutacce Musamman a ga Masu shiga tsarin Tajur Wakkar, shi Kuma Daya tsarin dama na mahaddata alqur’ani ne , Waɗannan su ne abubun da ake bukata kafin mu dauki dalibi”. Sheikh Elmulla

Yace akwai tsari na Musamman da suke tinanin fito da shi Musamman ga Waɗanda basu San Baki ba ,domin Suma su shiga Cikin Waɗanda zasu Mori alkhairin da Gidauniyar alFajr ta kawowa al’ummar Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kano Ta Zama Zakara A Jarrabawa NECO Ta Bana

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Najeriya (NECO),ta fitar...

Kungiyar Karamci United Family ta Karrama Shugaban gidan Radiyon Pyramid Saboda Taimakawa Al’umma

Shugaban gidan Radio tarayya Pyramid FM Dr. Garba Ubale...

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...