Bangaren Shari’a na taka muhimmiyar rawa wajen cigaban Mulkin Demokaradiyya – Osinbajo

Date:

Daga Zara Jamil Isa

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo yace fannin Shari’a na da gagarumar rawar da zai taka domin tabbatar da dorewar demokaradiyya a Fadin kasar nan.

Farfesa Osibanjo ya bayyana hakan ne yayin taron shekara-shekara na Kungiyar Malamai Lauyoyi ta Kasa Wanda aka Gudanar a Sabuwar jami’ar Bayero dake nan Kano

Farfesa Osibanjo yace kasashen Africa ne fama da barazanar hambarar da gwamnatocin siyasa, inda yace a yan shekarunan an Sami hambarar da zababbun gwamnatocin sama da 12  a kasashen frica ciki harda kasashen  Burkina Faso da kasar Mali da ya faru a baya bayanan.

Osibanjo yace duk da ana Kiran siyasar Najeriya a matsayin jaririya amma an sami nasarori ta hanyar  mika mulki a tsakanin zababbun gwamnatoci a kasar Ciki har yadda a shekara ta 2015  jamiyyar hamayya ta kada jam’iyya mai mulki, da kuma yadda ake baiwa tsagin Shari’a damar gudanar da aikinsu koda akan jam’iyya mai mulki.

 

Mataimakin Shugaban kasar yace wajibi ne dalibai da malaman sashin koyar da aikin Shari’a dake kasar nan su yi duba Kan cigaba da Kuma matsalolin da harkokin Damokaradiyya ke fuskanta kasancewar najeriya uwa a kasashen Africa.

Osinbajo taya Malaman Murnar zagayowar Wannan lokaci tare da fatan zasu. Cigaba da bada Gudunmawar da suke bayarwa domin cigaban fannin Shari’a a Kasar nan duk da Kalubalen da suke fuskanta.

A nasa jawabin Gwamnan jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa malaman sashin koyar da aikin Shari’a da suka shirya taron  a Jami’ar Bayero dake Kano, Wanda ya maida hankali Kan rawar da Sharia ke takawa Kan cigaban Damokaradiyya a Fadin kasar nan.

Daga bisani Ganduje ya yaba da irin rawar da bangaren Shari’a yake takawa wajen inganta harkokin Demokaradiyya a Kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kamata ya yi wajen Mauludi ya Zama waje Mai nutsuwa saboda ana ambaton Allah da Manzonsa – Mal Ibrahim Khalil

Shugaban Majalisar shuhurar Malamai ta jihar Kano Sheikh Malam...

Ra’ayi:‎Tsarin Kwankwasiyya ya dora Kano a gwadaben cigaba a mulkin Gwamna Abba Kabir -Adamu Shehu Bello

‎ ‎Ra’ayi ‎ ‎Daga Adamu Shehu Bello (Bayero Chedi), Jigo a Kwankwasiyya...

Al’ummar Garin Riruwai da wani Kamfanin Hakar ma’adanai Sun Cimma Yarjejeniya Kan Ci gaban yankin

Kwamitin ci gaban Al’ummar garajn Riruwai da wani kamfanin...