Siyasar Zamfara: Laifuka uku muka sami Mahdi Gusau da su ,babu abun da zai hana mu tsige shi – Yan Majalisar Zamfara

Date:

Daga Adam Bichi
 Majalisar dokokin jihar Zamfara ta ce ta mika wa mataimakin gwamna Mahadi Gusau sanarwar tsige shi ta hannun sakataren gwamnatin jihar.
 Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Honarabul Shamsudeen Bosko ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai matsayin majalisar jihar kan shirin tsige mataimakin gwamnan.
 Ya sha alwashin cewa babu abin da zai hana ‘yan majalisar dokokin jihar tsige mataimakin gwamna saboda an same shi da Laifuka har uku da ake zarginsa kuma in sun tsige shi za su maye kurbinsa da Mai kishin jihar.
 Zarge-zargen sun hada da karya kundin tsarin mulki, karya ka’idar ofishinsa da kuma almundahanar  kudade.
 ‘Yan majalisar sun yi ikirarin cewa Mataimakin Gwamnan ya saba wa sashe na 190 da 193  karamin sashe (1) (2)  A, B da C na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (kamar yadda aka yi masa kwaskwarima).
 Honorabul Bosko ya kuma jaddada cewa majalisar dokokin jihar Zamfara ta cika sharuddan sashe na 188 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) wanda kashi daya zuwa biyu bisa uku na ‘yan majalisar gaba daya sun amince da tsige Mataimakin Gwamnan.
 Sai dai babban sakataren mataimakin gwamnan, Umar Gusau a lokacin da Gidan Talabijin na AIT ya tambaye shi ko shugaban nasa ya samu sanarwar tsige shi daga majalisar dokokin jihar, ya ce ofishin mataimakin gwamnan bai samu wani sako daga majalisar ba.
 Ya kuwa Kara da cewa mataimakin gwamnan ta hannun lauyansa ya aike wa majalisar dokokin jihar Umarnin kotu Wanda ya hana ‘yan majalisar ci gaba da shirin tsige Mataimakin Gwamnan Jihar ta Zamfara.
Kadaura24 ta rawaito Dangantakar mataimakin gwamna Mahadi Aliyu Gusau ta yi tsami ne bayan da mai gidan sa gwamna Bello Mohammed ya koma jam’iyyar APC a shekarar da ta gabata, yayin da mataimakinsa ya ci gaba da zama a jam’iyyar PDP tare da shugaban ma’aikata, Kanar Bala Mande ya yi ritaya da sauran Wasu jiga-jigai a Jam’iyyar PDPn dakeJihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...