Daga Halima M Abubakar
Wata kotu a Jihar Kano ta umarci jami’an tsaro da su ci gaba da tsare Mu’azu Magaji, tsohon kwamashinan ayyuka, bisa zargin ɓata sunan Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje.

Mai Shari’a Aminu Gabari na kotun da ke Nomansland a Kano ya kuma umarci a aika likitoci su duba lafiyar shahararren mai sukar Gwamna Ganduje wanda aka fi sani da Ɗan-Sarauniya ko kuma Win Win.
Kazalika, alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 3 ga watan Fabarairun 2022.
Ya umarci lauyoyi masu shigar da ƙara da kuma masu kare wanda ake zargin da su kawo masa kundin shari’ar a ranar