Gwamnatin kano ta ragewa ‘yan adaidaita sahu kudin sabunta rigista zuwa 5,000

Date:

Daga Rukayya Abdullahi maida

Gwamnatin jihar Kano ta hannun Hukumar KAROTA ta cimma matsaya tsakaninta da matuƙa Baburan Adaidaita Sahu waɗanda suka tafi yajin aiki makon da ya gabata dangane da ƙalubalantar Gwamnatin na rage musu kuɗin sabunta Takardar Tuƙi daga Naira Dubu Takwas.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jamaa na Hukumar KAROTA Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya sanyawa hanu ya kuma aikowa kadaura24 ta ce a zaman na yau ya gudana ne a ofishin Uwar Ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa reshen jihar Kano.

Bayan shafe fiye da awanni huɗu ana tattaunawa da ɓangarorin, ta hannun Lauyansu Barista Abba Hikima Fagge da Wakilin Gwamnatin jihar Kano Hon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi Shugaban Hukumar KAROTA da Gamayyar halastattun ‘Yan Ƙungiyoyin Adaidaita Sahu na jihar Kano.

A zaman na yau an amince da ragewa matuƙa Baburan Adaidaita Sahun biyan kuɗin shaidar tuƙi Permit sabo daga Naira Dubu goma Shata kwas (18,000) zuwa Naira Dubu Goma Sha biyu (12,000), sabunta wa kuma daga Naira Dubu Takwas (8,000) zuwa Naira Dubu Biyar 5000.

Zaman ya amince da biyan harajin kulum-kullum har da ranar Lahadi, wanda a baya sai dai su biya kuɗin ranar Lahadi a ranar Litinin,

Haka kuma zaman ya amince kuwanne Ɗan Adaidaita Sahu ya biya wannan kuɗi nan da ƙarshen watan biyu na Febreru na wannan shekarar, ƙin biyan kuɗin a wannan lokacin zai sai a biya kuɗin baya kamar yadda zaman ya amince.

An gudanar da zaman ne a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi na jihar Kano Barista Aminu Sani Gadanya

A nasa jawabin wakilan Gwamnatin jihar Kano kuma shugaban Hukumar KAROTA Dr. Baffa Babba Dan’agundi ya yabawa shugaban Rundunar tsaro ta farin Kaya wanda bisa ga gudummawar da ya bayar ne aka samu wannan matsaya, Sannan ya bayar da tabbacin Hukumar KAROTA da matukar Baburan adaidaita sahun sun sami kyakkyawar fahimtar juna a lokacin da suke gudanar da tuƙi a kan titi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...