Daga Hussaini Kabir minjibir.
Gobara ta ƙone kaya da abinci da kuɗin su ya haura Naira miliyan uku da rabi a unguwar lokan maƙera ƙaramar hukumar Gwale dake birnin Kano.
Da yake jawabi ga manema labarai don gane da musababbin tashin gobarar, mai gidan malam sulaiman Abdullahi lokon makera ya bayyana cewa wutar ta tashi da misalin ƙarfe biyu na rana sakamakon wutar lantarki mai ƙarfi.
Inda yace wutar ta ƙone kayan sawa da kayan abinci da muhimman takardu da rufin ɗakuna guda huɗu.
Kadaura24 ta rawaito cewa ba a samu asarar rai ba kuma babu wanda ya sami rauni.
Tuni dai Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar Dr. Sale Aliyu jilli ta ziyarci gidan da akai gobarar har kuma ta bashi gudunmawar kayan abinci da kayan rufin kwano da siminti da katifu domin rage masa raɗadi.
Ta kuma jajanta masa a madadin gwamnatin jihar Kano.
Ta kuma yi kira ga sauran al’umma da su dinga kiyaye wa da kayayyakin wuta musamman a wannan lokaci na hunturu.