Daga Umar Hussain Mai Hula
Yan Kannywood sun tabbatar da goyon bayan ga takarar Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura a Matsayin Wanda zasu saka a gaba Idan zaben Gwamnan Jihar Kano yazo a Shekara ta 2023.
Wanda ya shirya taron kuma fitaccen jarumin Kannywood T.Y Shaba ne ya bayyana haka jim kadan bayan karrama dan takarar.
Shaba ya ce AA Zaura Muka zabe ya zama dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar APC .
Wannan dai na zuwa ne shekara guda gabanin babban zaben Shekara ta 2023 .
Ya ce goyon bayan A A Zaura ya zama dole idan aka yi la’akari da yawan nasarorin da ya samu da ci gaban da ya kawowa al’umma, da ayyukan alheri da yake yi wa al’ummar jihar Kano ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.
Da yake jawabi tun da farko, Jarumin masana’antar Kannywood, Sharif Aminu Ahlan, ya ce zasu nuna cikakken goyon baya ga takarar Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura duba da yadda ya fara da kuma imaninsu idan ya zama gwamnan jihar zai taimaka wa masana’antar ta Kannywood.
“Ya bambanta a cikin mutanen da ke neman kujerar Gwamna, kuma muna da tabbacin zai kawowa kano cigaba idan aka ba shi goyon baya a lokacin babban zabe na 2023″. Inji Ahlan
“Tabbas burin mu na kafa film village zai tabbata Idan Zaura ya zama Gwamnan Kano tunda har yanzu Tsare-tsaren mu na ganin hakan suna kasa”.
“Akwai bukatar malamai su fahimci fa’idar da ke tattare da kafa irin wadannan cibiyoyi na Film Village ta hanyar samawa da yawa daga cikin matasanmu aiki yi, Wanda yin hakan zai rage yawan laifukan da matasan Kan yi”. Inji Ahlan
Jarumin ya kara da cewa sun zabi A. A Zaura ne, saboda aminta da cewa zai aiwatar da shirye-shirye da ayyukan da suke da shi na bunkasa masana’antar.
“Shekaru da dama muna cikin wannan tafiya ta Siyasa, kuma ‘yan takara da dama sun yi amfani da mu ta hanyar tallata su da alkawuran idan suka ci zabe zasu tallafa Mana, amma idan suka hau mulki, to shikenan sai su manta da mu”. Sharif Aminu Ahlan.
A Jawabinsa Mai neman zama dan takarar kujerar gwamnan jihar kano A jam’iyyar APC, Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura, ya yaba da irin wannan karamcin da Jaruman Kannywood din suka yi masa, kuma ya yi alkawarin cika dukkan burinsu idan hakar sa ta cimma Ruwa.
A.A Zaura ya ce lokaci ya yi da jama’a za su karrama jaruman fina-finai duba da irin gudunmawar da suke baiwa al’umma ta fuskar zamantakewa da tarbiyya.
Sai dai yayin taron yan jaridu sun fuskanci kalubale wajen shiga cikin dakin taron musamman daga bangaren yan tawagar A A Zauran Wanda kuna ba su suka shirya taron ba kuma ba su suka gayyaci manema labaran ba.