Farfesa Gwarzo Ya Mika Ta’a’ziyyarsa Bisa Mutuwar Ma’aikacinsa Robert Fanen Terwase

Date:

Daga Ali kakaki
Shugaban Rukunin Jami’o’in Maryam Abacha American University dake kasashen Nijeriya da Nijar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bayyana rasuwar daya daga cikin ma’aikatansa Robert Fanen Terwase da cewa rashi ne  babba ga jami’ar saboda hazikin ma’aikaci ne.
Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya yi wannan bayanin ne a cikin wata takardar sakon ta’aziyya mai dauke da san hannunsa zuwa ga iyalan mamacin a yau Lahadi 8 ga watan Janairun 2022.
“A madadin ni kaina da iyalaina da daukacin ma’aikatan dake karkashina, muna mika ta’aziyyarmu ga ‘yan’uwa da abokan arziki musamman iyalan Marigayi Robert Fanen Terwase kan rashinsa, a don haka ina addu’ar Allah madaukakin Sarki da ya baiwa iyalinsa juriyar wannnan “, inji Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo.  
Marigayiya Robert Fanen Terwase ya bar duniya a ranar Asabar yana da shekaru 46, ya bar mace daya da ‘ya’ya 4.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...