Gwamnatin Tarayya ta Kara Harajin Naira 10 a Duk Kwalbar Lemo

Date:

Gwamnatin Najeriya ta ƙara harajin naira 10 kan duk wata lita da duka lemukan kwalba da ba giya ba, da sauran wasu lkayayyakin kwalama.

Wannan sabuwar dokar ma dauke ne cikin dokar kudi ta gwamnati ta 2021.

A cewar dokar an sanya wannan haraji ne domin rage yawan shan sikari wanda yake janyo ciwon siga da kuma kiba, da dai wasu abubuwan na daban.

Ministar kudi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ta ce an samar da wannan karin kudin ne kan abubuwan da ke janyo rashin lafiya da kashe kudade ba bisa dalili ba.

Cikin kayayyakin da abubuwan suka shafa akwai Coca-Cola, Pepsi, Sprite da sauran abubuwan da suke janyo kiba saboda zakin da suke da shi.

BBC Hausa ta rawaito Rahotanni sun ce akwai kimanin ;’yan Najeriya miliyan hudu da ke fama da ciwon siga wanda ke da alaka kai tsaye da yawan shan siga da suke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Korar ma’aikata a Kano: Bashir Gentile ya yiwa Faizu Alfindiki martani mai zafi

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Masanin kimiyar siyasa kuma mai sharhi...

Sakataren kungiyar NRO Abdulkadir Gude ya rasu

Allah ya yi wa dattijo, kuma Sakataren kungiyar Northern...

Gwamnatin da ta ke korar Ma’aikata ba ta Cancanci Wa’adi na biyu ba – Faizu Alfindiki

Daga  Maryam Muhammad Ibrahim   Abin takaici ne ganin yadda gwamnatin...

Zaizayar kasa: Gwamna Abba gida-gida ya raba diyyar Naira Miliyan 600 A Kano

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...