Ma’aikatar Harkokin Mata, Yara da Mutanen da ke da Bukatu na Musamman ta Jihar Kano ta jinjinawa ƙungiyar ’Yan Jarida Mata ta Najeriya (NAWOJ), reshen jihar Kano, bisa jajircewarsu wajen inganta lafiyar mata, ƙarfafa su, da kuma wayar da kan al’umma.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa Mai dauke da sa hannun shugabar kungiyar Bahijja Malam Kabara da mataimakiyarta Aisha Muhd Yanleman, kuma aka aikowa Kadaura24.
Sanarwar ta ce Kwamishinar ma’aikatar, Hajiya Amina Abdullahi Hod, wacce Hajiya Nafi Muhammad Yakasai ta wakilta, ce ta yaba wa NAWOJ bisa shirye-shiryen da suke gudanarwa, musamman taron bita da wayar da kai ga manbobinsu kan cutar sankarar mama.

Haka kuma, ta mika godiya ga gidauniyar Aminu Magashi Foundation (AMG) bisa daukar nauyin taron wayar da kan Sankara mama da goyon bayan shirye-shiryen kula da lafiyar mata a faɗin jihar. Ta ce tallafin da gidauniyar ke bayarwa yana taimakawa sosai wajen ƙara kusantar da bayanan lafiya ga mata .
NURTW ta Karrama DMD Karota Auwal Aranposu
Hajiya Nafi ta kuma yi godewa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayansa ga al’amuran da suka shafi mata, yara, da masu buƙatu na musamman.
A nata bangaren, Shugabar kungiyar NAWOJ ta jihar Kano, Comrade Bahijja Malam Kabara, ta gode wa Ma’aikatar Mata bisa hadin kan da take baiwa kungiyar da kuma yadda take tallafawa mata da kananan yara a kano.
Ta tabbatar da cewa NAWOJ za ta ci gaba da gudanar da ayyukan wayar da kai kan matsalolin da suka shafi mata tare da hada kai da gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu domin inganta rayuwar mata da yara a Kano.