Tsoffin Kwamishinonin Kano sun Musanta labarin goyon bayan Sanata Barau a 2027

Date:

Kungiya ta tsoffin kwamishinoni da suka yi aiki a gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta musanta wani rahoto da ya yaduwa a kafafen yada labarai, wanda ke cewa sun amince da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, a matsayin ɗan takarar gwamna na 2027 a Kano.

Kungiyar ta bayyana rahoton a matsayin maras tushe Wanda kuma aka kirkir da nufin yaudarar al’umma.

Da yake jawabi a madadin kungiyar, tsohon Kwamishinan Harkoki na Musamman kuma ɗan takarar kujerar shugaban APC na Kano, Alhaji Dr. Mukhtar Ishaq Yakasai, ya ce kwata-kwata ba su tattauna wata magana Mai alaka da nuna goyon bayan Sanatan ba.

InShot 20250309 102512486

Dr. Yakasai ya bayyana cewa kungiyar ta ziyarci Sanata Barau ne bayan da ya gayyace su, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi bunkasa jam’iyya, ƙarfafa haɗin kai da cigaban ƙasa.

Ya kuma ce jam’iyyar APC a Kano tana da jagoranta Abdullahi Umar Ganduje, sannan da shugaban jam’iyya na jiha, Abdullahi Abbas za su bi tsarin jam’iyya wajen zaɓen wanda zai tsaya takara.

Kungiyar Iyayen Daliban MAAUN Ta Karyata Koken da Aka Kai wa PCACC, Ta Ce Jami’ar Na Da ‘Yancin Kanta

“Ni da na ke neman kujerar shugaban APC na jihar Kano, ta yaya za a ce na amince da mutum ɗaya? Bayan Akwai A.A. Zaura, Murtala Sule Garo, tsohon mataimakin gwamna Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, da wasu ma da za su fito, ta Yaya za a ce mun zabi mutum ɗaya?”

Ya yi kira ga mambobin jam’iyya da al’umma da su yi watsi da labarin, yana mai cewa labari ne na bogi da aka Samar da shi da nufin tada fitina a cikin jam’iyya.

Kungiyar ta ce tana nan daram wajen mara wa APC baya a jihar, tare da Mata baya ga duk wanda jam’iyyar za ta tsayar takara a 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...

NUC ta kakabawa jami’o’i takunkumi kan yadda suke ba da digirin girmamawa a Najeriya

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta sanar...

Kungiyar Iyayen Daliban MAAUN Ta Karyata Koken da Aka Kai wa PCACC, Ta Ce Jami’ar Na Da ‘Yancin Kanta

Shugaban Kungiyar Iyayen daliban  jami’ar MAAUN, Alhaji Mustapha Balarabe,...