Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta samu jagoran ƙungiyar ƴan aware ta Biafra, Nnamdi Kanu da laifuka bakwai da ake tuhumar sa da aikatawa masu alaƙa da ta’addanci.
Alƙalain da yake shari’ar, Mai Shari’a James Omotosho ya ce masu gabatar da ƙarar sun tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi wa Nanamdi Kanu.
Tuhume-tuhumen da ake yi wa Kanu sun haɗa da ta’addanci da tunzura jama’a su kashe ƴan sanda da kasancewa mamba a haramtacciyar ƙungiyar IPOB da gwamnatin Najeriya ta haramta da kuma yaɗa farfagandar ta’addanci.
Mai Shari’a Omotosho ya ɗage zaman na wani ɗan lokaci inda ya ce zai yanke wa Nnamdi Kanu hukunci idan aka koma nan ba da jimawa ba.

Ana sa ran wannan ya kawo ƙarshen kimanin shekara 10 da aka kwashe ana shari’a, tun bayan da gwamnati ta gurfanar da shi.
Mai shari’ar James Omotosho ya ce zai yanke hukuncin ne a yau bayan Kanu ya gaza kare kansa duk da damar da aka ba shi.
A watan Maris ne Omotosho ya karɓi jagorancin shari’ar, inda ya fara daga farko, bayan jagoran na IPOB ya zargi tsohuwar alƙaliyar da ke shari’ar, Binta Nyako da rashin adalci, sannan ya buƙaci ta tsame kanta daga shari’ar.
Abubuwan da suka faru
Tun bayan karɓar shari’ar, Omotosho ya bayar da umarnin hanzarta kammala shari’ar.
Mai shari’a a Omotosho ya bai wa lauyoyin gwamnatin Najeriya wa’adin kwanakin da za su gabatar da duk tuhume-tuhumensu, da gabatar da shaidu da kammala duk wani ƙorafi da suke da shi.
Babban Lauyan Najeriya, Adegboyega Awomolo, wanda shi ne jagoran lauyoyin gwamnatin Najeriya ya kamala gabatar da shaidu da tuhume-tuhume kamar yadda alƙalin ya umarta.
Tawagar gwamnatin tarayya ta kammala gabatar da shaidu da hujjojinta ne a ranar 19 ga watan Yunin 2025.
Daga cikin abubuwan da suka gabatar sun haɗa da bidiyoyi da sautukan da aka naɗa na bayanan Nnamdi Kanu, ciki har da inda yake umurtar mabiyansa su kai farmaki da kuma kashe sojoji da ƴansandan Najeriya, da lalata kadarorin gwamnati, da kuma inda yake yi wa mutanen kudu maso gabashin Najeriya barazana idan suka ƙi yin biyayya ga dokarsa ta zama a gida.
A nata ɓangaren, tawagar lauyoyin Nnamdi Kanu, ƙarƙashin jagorancin tsohon ministan shari’ar Najeriya Kanu Agabi, daga farko sun gabatar da buƙatar cewa kotu ta zartar da hukuncin cewa babu wani laifi da Kanu ya aikata kuma babu buƙatar ya gurfana a kotu.
Sun buƙaci kotun ta yi watsi da duk wasu tuhume-tuhume da ake yi masa, domin a cewarsu babu wata hujja ta gurfanar da shi.
Sai dai mai shari’a Omotosho ya yi watsi da batun nasu, inda ya ce akwai buƙatar Kanu ya gurfana a kotu domin bayar da bahasi kan wasu shaidu da aka gabatar a kansa.
Daga lokacin ne tsarin tafiyar da shari’ar ya fara tabarɓarewa.
Da farko, Nnamdi Kanu ya kori lauyoyinsa sannan ya ce shi ne zai kare kansa.
Bayan ba shi lokaci domin duba takardun tuhume-tuhumen da ake yi masa da kuma shirya yadda zai kare kansa, a zama na gaba Kanu ya shaida wa kotu cewa babu halasci a tuhume-tuhumen da ake yi masa, saboda haka babu bukatar ya kare kansa.
Kanu ya dage kan cewa dokokin da lauyoyin gwamnati suka dogara da su wajen tuhumarsa tsofaffin ne waɗanda aka soke, saboda haka ya buƙaci alƙali ya sake shi, ya yi tafiyarsa.
Daga nan ne alƙalin ya shaida wa Kanu cewa an wuce matakin yin muhawara kan abubuwan da yake magana a kai, amma ya ce zai yi la’akari da su a lokacin yanke hukunci, sannan ya shawarce shi da ya gabatar da hujjojinsa na kariya daga tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Bayan ɗage shari’a sau shida, inda a duk wannan lokacin mai shari’a Omotosho ya riƙa shaida wa Nnamdi Kanu haɗarin rashin gabatar da hujjojin kare kansa, sai alaƙalin ya yanke hukuncin cewa Kanu ya rasa damar da yake da ita ta kare kansa.
Kwanaki kaɗan bayan haka sai Nnamdi Kanu ya shigar da ƙara a kotun daukaka ƙara yana buƙatar a dakatar da babbar kotun daga shirinta na yanke hukunci har sai ta saurari ƙorafinsa na cewa dokokin da aka dogara da su wajen tuhumarsa tsofaffi ne da aka daina amfani da su.
Ɗaya daga cikin tsofaffin lauyoyin Nnamdi Kanu ya shaida wa BBC cewa bisa la’akari da shari’ar da Kanu ya shigar a kotun ɗaukaka ƙara, babban kotun da ke shari’ar Kanu ba ta da wata dabara face ta jira har sai kotun ɗaukaka ƙara – wadda ke sama da ita – ta yanke hukunci.
Sai dai wani lauyan, wanda ke da masaniya kan shari’ar ya shaida wa BBC cewa ƙarar da Kanu ya shigar a kotun ɗaukaka ƙara ba za ta hana mai shari’a Omotosho yanke wa Kanu hukunci ba a ranar 20 ga watan Nuwamba da ya ayyana.
Lauyan ya ce ƙarar da Kanu ya shigar a kotun ɗaukaka ƙara ba a kan wani hukuncin kotu da aka yanke ba ne, saboda haka kotun ɗaukaka ƙara ba za ta iya umurtar a dakata da yanke hukunci ba.