Hana Barace-Barace a Kano: Ku Koyawa Mabaratan Sana’o’i don inganta Rayuwar su – Sarkin Bichi

Date:

Daga Zara Jamil Isa
 Mai martaba Sarkin Bichi a Kano, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta samawa masu bara a tituna sana’o’i don su zama masu dogaro da kawunansu kafin hana su barace-barace.
 Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da kwamitin da ke kula da kwashe mabarata a tituna da Mai dasu gida na jihar ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa.
Sarki Bayero ya ce idan ana so a kawar da barace-barace don inganta rayuwarsu, dole ne a baiwa mabaratan hanyoyin da zasu inganta tattalin arziki.
 Sarkin ya bukaci kwamitin da ya wayar da kan jama’a kan jama’a kan illar barace-barace a tsakanin al’umma.
 Ya kuma umurci dukkan masu unguwanni da Dagatain  masarautarsa ​​da su marawa kwamitin baya a aikin da yake na magance matsalolin zamantakewa.
Shugaban kwamatin, Alhaji Rabi’u Suleiman ya ce sun kasance a fadar ne domin sanar da sarkin irin shirye-shiryen kwamitin da kuma neman goyon bayansa da kuma albarkarsa domin kawo karshen barace-barace a jihar.
Cikin wata sanarwa da Mamba Kuma Wakilin Ma’aikatar yada labarai ta Jihar Kano Sani Abba Yola ya aikowa Kadaura24 yace Bichi wanda ya samu wakilcin Manajan Daraktan hukumar hana barace-barace da mai da su gida, Malam Muhammad Albakary Mika’il ya bayyana cewa kwamitin ya tuntubi dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabannin kungiyoyin farar hula da Shugabanin yada labarai da Malamai da dai sauransu.
 Manajan daraktan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yanke shawarar kafa kwamitin ne sakamakon kudurin da gwamnonin jihohin arewa suka dauka na hana barace-barace a yankin.

6 COMMENTS

  1. Wonderful blog! I found it while browsing on Yahoo News. Do youhave any suggestions on how to get listed in Yahoo News?I’ve been trying for a while but I never seem to get there!Appreciate it

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...