Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da daftarin kasafin kudin jihar na shekarar 2026 Wanda ya kai N1,368,127,929,271 ga Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Yayin da yake jawabin a gaban Majalisar dokokin jihar Kano gwamnan ya nanata kudirin gwamnatinsa na kammala manyan ayyukan da gwamnatisa ta gada domin cigaba al’umma.
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa Kadaura24,

Ya ce an warewa Manyan aiyuka kaso mafi tsoka ya kunshi kaso mafi girma na kasafin kudin, wanda ya kai N934.6 biliyan. Sai kuma kashi 32 cikin ɗari na kudaden gudanarwa da suka kai Naira bilinyan N433.4
Gwamna Yusuf ya ce fannin Ilimi ya samu kaso mafi tsoka na N405.3 biliyan (30%), sai Ayyukan Raya Kasa da aka ware musu Naira N346.2 biliyan (25%), sannan bangaren Lafiya aka ware masa Naira N212.2 biliyan (16%).
Nazarin Yadda Shaharar Sanata Barau Ta Karade Nigeria – Abba Anwar
“Wannan kasafin ya nuna aniyar mu ta ci gaba da gina ɗan Adam, ta hanyar inganta ilimi da lafiyar jama’a, tare da shimfida tubalin cigaba mai ɗorewa a jihar,” in ji shi.
Ya ce bangaren tattalin arziki da walwalar Jama’a su ne suka fi samun kaso mafi tsoka na daftarin kasafin na 2026, wadanda suka hadar da Noma, Tsaro, Kasuwanci, Ruwa, Muhalli, yawon bude ido, ci gaban mata da matasa, da kuma kula da masu bukata ta musamman.
Ya bukaci ’yan majalisar da su hanzarta amincewa da kudirin kasafin, domin a fara aiwatar da shi akan lokaci don cigaban jihar Kano .