Daga Abba Anwar
Wani babban abin lura game da rayuwar siyasar mataimakin shugaban majalisar dattawa ta kasa, Sanata Barau Jibrin CFR, shine, yadda wasu dake masa kallon su sa’o’insa ne a siyasa, alhali kuwa karansu ko kadan bai kai tsaiko ba.
Shi dai tun ma fa a zamanin Jamhuriya ta biyu, wato lokacin tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kano, Muhammadu Abubakar Rimi, Barau yake fitacce kuma wayayye kan harkar siyasar kasa ba ma ta jiha kawai ba. A lokacin fa wadanda a yanzu suke masa kallon shi sa’ansu ne, ko kusa da kafarsa ba su kai ba.
Saboda haka tun farkon farawa ma daga lokacin da mulkin dimukuradiyya ya dawo a shekarar 1999, bayan dadewa da a ka yi cikin mulkin soja, shi ba kifin rijiya ba ne.

A wancan lokacin na 1999 ya samu cin nasarar zama dan majalisar wakilai ta kasa, mai wakiltar karamar hukumar Tarauni, cikin birnin Kano.
Majalisar tarayya ta yanzu fa, bayan dawowar mulkin farar hula, ta samo tsayawa da kafar ta ne fa sakamakon yadda su Barau a wancan lokaci su ka tafiyar da harkar majalisar. Idan ka yi nazarin irin ayyukan jajircewa da ya yi a waccan majalisa, za ka san ashe dama can shi gwarzon dan siyasa ne.
A majalisar 1999 zuwa 2003, shine shugaban kwamitin rarraba dukiyar kasa, wato Appropriation Committee, lokacin marigayi Ghali Umar Na’Abba shine Kakakin majalisar wakilai din.
Tun fa da jimawa ma kafin dawowar mulkin farar hula a 1999, Barau wayayye ne, kwararre, dan siyasa mara tsoro, mai jajircewa kuma wanda yake da shaidar biyayya ga shugabanni da shugabanci.
Amman idan mutum ya na son sanin waye Barau a siyasar gidan tsohon gwamna Rimi ko ma a siyasar dake da alaka da marigayi Malam Aminu Kano, wato tun ma kafin 1999 kenan, to mutum ya tuntubi mutane irin su tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ko Hamza Darma ko Dauda Raula ko Aminu Nasidi ko Aminu Babba Dan Agundi, Sarkin Dawaki Babba a masarautar Kano da dai ire-irensu, jajirtattu ‘yan siyasar gaba-dai-gaba-dai.
Ai kuwa daga lokacin da ya zama Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa kuma, ya nuna kwarewa da jajircewa wajen tafiyar da ayyukan sa na majalisa. Dama ya shiga a matsayin wayayye, wanda kuma ya saba da siyasar kasa gaba daya. Shi fa gogewarsa da tasirinsa ba su tsaya kan mazabar sa kawai ba.
A na nan a na nan har ya zama an zabe shi a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa ta kasa. Su kan su abokan aikinsa sun lura da irin hobbasarsa wajen tafiyar da ayyukan majalisa da sanin yakamatan sa da kuma kishin kasar sa wajen ganin an samu daidaito da kuma hadin kan kasa.
Cikin Ikon Allah sau da yawa kuma ya na tsallake makirce-makirce da a ka kulla masa ba daya ba ba biyu ba ba uku ba. Amma cikin kiyayewar Allah, sai ya kasance kullum sai kara gaba yake cikin al’amuransa. Dama haka hanyar samun nasara take cike da samun cikas da hawa-da-sauka. Wasu lokuta na ba gaira-ba-dalili.
Kuma ya na kokarin gaske wajen ganin bai ba mazabarsa ta Kano ta Arewa da kuma jihar sa kunya ba, ta yadda yake gabatar da kudurori masu amfanin gaske ga majalisa. Wasu ma daga cikin kudurorin wadanda za su tallafawa ci gaban kasa ne kai tsaye. Baya ga na wadanda su ka shafi mazabarsa da jihar sa, da kuma nahiyarsa ta Arewa.
Wasu a tasu mahangar Sanata Barau fa ya samu wadannan damammaki ne saboda kujerar da yake kai ta mataimakin shugaban majalisar dattawa. Sau da yawa za a iya ce musu wannan gaskiya ne. Haka abin yake. Saboda ya kamata su ma su gane cewar a dalilin matsayin da yake kai din kuwa, to shi ba sa’ansu ba ne. Ba tsaransu ba ne. Saboda haka hada kai da shi da tunanin wai shi sa’an kowa ne, to tamkar karo ne da wani murgujejen dutse mai firgici. Kamar dai tarar aradu da ka.
Tun da babban burin wannan rubutun shine ya kawo yadda Sanata Barau ya yi shuhura kuma ya yi zarra a siyasar kasa gaba daya, ba wai iyakacin ta mazabar da yake wakilta ba, ko ta jihar Kano kawai, saboda haka ba zan tsomo batuttukan da su ka shafi abubuwan cigaba da more rayuwa da yake aiwatarwa a jihar Kano kawai ba.
Zan dan tsallaka na kawo kadan daga cikin kadan na ire-iren kudurorin da yake mikawa majalisa da su ka shafi cigaban wasu yankuna na kasar nan. Shi fa dan siyasa ne kuma abin alfahari ga kasa gaba daya, ba wai iyakacin dan tsukin da yake wakilta ba.
Kadan daga cikin ire-iren dokokin da majalisar dattawan ta yi sakamakon kudurorin da ya mika ga majalisar sune kamar haka, “Cyber Crimes (Prohibition, Prevention, etc) Bill (2023), Federal College of Education (Technical), Aghoro Bill (2019), in Bayelsa state, College of Mines and Geological Studies, Guyuk, Bill (2019), Federal University of Aquatic Studies, Ogharu, Bill (2019), in Anambra state and University of Maritime Studies, Oron, Bill (2017), Development Planning and Projects Continuity Bill (2023).”
Kuma fa a dalilin yadda ya zama ya shahara kan siyasar kasa gaba daya, tare da kasancewarsa shugaba nagari hakan ta sa a na gayyatarsa wasu al’amurran da su ka shafi wasu bangarorin kasar nan dan ya samu ya halarta kuma ya sa musu albarka.
Misali kwanan nan ya halarci bikin wani bikin shekara shekara da a ke yi na shekarar 2025 na Oronna Ilaro a jihar Ogun. Wanda ya je bikin ne tare da wasu manyan Sanatoci da su ka fito daga yankin. Wannan shi yake nuna maka yadda suke girmama shi a majalisar dattawa. Mutum ne mai salon shugabanci nagari.
Kuma a dalilin shi Sanata Barau din an samu wasu muhimman baki daga kasashen waje zuwa wajen bikin. An yi bikin ne a Asade Agunloye Pavilion Ground in Ilaro-Yewa, jihar Ogun. Shi Olu of Ilaro babban mai sarauta na Yewaland, His Royal Majesty, Oba (Dr) Kehinde Gbadewole Olugbenle, shine wanda ya shirya bikin.
Daga nan kuma ya karasa zuwa jihar Lagos dan taya tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Wannan fa duk a na nuni da cewar shi fa Sanata Barau mutum ne da ya yi fice a dukkan bangarorin kasar nan. Ba wai a waje daya kawai yake da kima da mutunci ba.
A dalilai irin wadannan ne ya sa har babbar jaridar nan ta kudancin Najeriya wato The Sun ta yi nazari ta gano ayyukan alheri da kuma tasiri da Sanata Barau yake da shi a siyasar Najeriya, har su ka zabe shi a matsayin wani babban mutum da za su karrama a karshen watan Janairu na shekara nai shigowa ta 2026. A can jihar Lagos.
An san hakan ne lokacin da Manajan Darakta na kamfanin jaridar Mr Onuoha Uke ya ja ragamar shugannin gidan jaridar kwanan nan zuwa ga ofishin Sanata Barau din har su ka shaida masa hakan. Sunan wannan girmamawa da za su yi masa ita ce, “The Sun Humanitarian Service Icon Award 2025.”
Saboda haka fa shi Sanata Barau ba sa’an wasu ba ne masu ganin ya tsone musu ido. Ba tsaran masu tasowa ba ne. Ko ma wadanda sun taso din amma ba su da kowane irin tasiri a tsarin siyasar jiha balle ma a ce ta kasa gaba daya. Shi din nan dai haka Allah Ya yi shi. Ba abinda ya rage ga abokan siyasa sai kallo. Yadda Ubangiji Ya tsara haka tsarin ke tafiya.
Anwar ya rubuta wannan daga Kano
Laraba, 29 ga Nuwamba, 2025