Gwamnatin Najeriya ta amince da biyan ‘yan sandan kasar sabbin kudaden alawus wadanda za su sa albashin da suke dauka ya karu da kashi 20 cikin 100.
Ministan harkokin ƴan sanda na kasar Muhammadu Maigari Dingyadi ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron majalisar zartarwar kasar na mako-mako da aka yi a jiya.
A cewar ministan ‘yan sandan, za a fara biyan wannan sabon tsarin biyan alawus na musanmman wanda majalisar zartarwa ta amince da shi ne a watan janairun 2022; wato watan gobe kenan.
Ya ce waɗannan kudaden alawus za su kara yawan albashin jami’an ‘yan sanda a kasar da kashi 20 bisa dari.
BBC Hausa ta rawaito Ministan ya ce ƙarin albashin wani bangare ne na kokarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi na biyan bukatun da masu zanga-zangar EndSars suka gabatar.
Taron majalisar zartarwar wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ya kuma amince da yi wa ‘yansandan ƙarin ga kudaden alawus na kwanan daji wato duty tour allowance da kashi shida bisa dari
כחלק מהשירות, אנו מעניקים משלוחים בכל הארץ עד לבית הלקוח ושומרים עבורך על דיסקרטיות מלאה. דירות דיסקרטיות במרכז