Ramadan: Kungiyar Matasan Nyako ta Rabawa Yan Gudun Hijira kayan Abinchi a Adamawa

Date:

Daga Zayyad Isma’il Yola

Wata kungiyar matasa dake goyon bayan tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala H Nyako a yau ta raba kayan abinci ga ‘yan gudun hijirar da ke yola.


 Kungiyar wacce aka fi sani da Nyako Supporters Group ta raba katan 50 na spaghetti ga ‘yan gudun hijirar a kokarin su na rage wahalar’ da yan gudun hijirar suke fuskanta.


 Yayin Isar da kayayyakin mukaddashin shugaban kungiyar Abubakar Jalo Elhaps ya ce dalilin kai tallafin shi ne don rage radadin da ‘yan gudun hijirar ke ciki da kuma sanin irin gudummawar da jagoran su na siyasa Admiral Murtala H. Nyako ya bayar wajen bunkasa ayyukan jin kai ga mutanen jihar Adamawa musamman mata da matasa a lokacin  lokacin da yake gwamnan jihar Adamawa.


 Abubakar ya ci gaba da cewa mambobin kungiyar suna hada abun taimakon ne da kansu don ba da gudummawar kudi wajen gudanar da wannan shirin.


 Don haka ya yi kira ga gwamnatin jihar Adamawa da ta yi koyi da Manufar Baba Mai Mangoro da kudirorinsa na kyautata Rayuwar Matasa l domin magance matsalolin da babban birnin jihar ke fuskanta musamman ‘yan Shila
 Da yake karbar kayayyakin abincin, shugaban ‘yan gudun hijirar na malkohi Mista Lawrence Weda ya gode wa kungiyar ta Nyako bisa ga namijin kokarin da suka yi na yin la’akari da sansanin’ yan gudun hijirar na Malkoyi.


 Ya kara bayyana matasan a matsayin jakadu na kwarai tare da karfafa gwiwar sauran matasa suyi koyi da su.


 Kadaura24 ta rawaito cewa Idan za a iya tunawa, an kafa kungiyar tallafawa Nyako ne a shekarar 2015 da zimmar kare manufofi da shirye-shirye na tsohon gwamna Murlata H Nyako don tabbatar da cigaba mai dorewa

63 COMMENTS

  1. Allah yakyauta kuma yatallawa jagororin wannan qungiya dashikansa wanda muke koya agareshi abinnufi Murtala Hamman yero Nyako

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Korar ma’aikata a Kano: Bashir Gentile ya yiwa Faizu Alfindiki martani mai zafi

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Masanin kimiyar siyasa kuma mai sharhi...

Sakataren kungiyar NRO Abdulkadir Gude ya rasu

Allah ya yi wa dattijo, kuma Sakataren kungiyar Northern...

Gwamnatin da ta ke korar Ma’aikata ba ta Cancanci Wa’adi na biyu ba – Faizu Alfindiki

Daga  Maryam Muhammad Ibrahim   Abin takaici ne ganin yadda gwamnatin...

Zaizayar kasa: Gwamna Abba gida-gida ya raba diyyar Naira Miliyan 600 A Kano

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...