Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir ya rantsar da Barr. Abdulkarim Kabir Maude a matsayin sabon kwamishinan Sharia kuma babban lauyan gwamnatin jihar Kano.
Kazalika gwamnan ya rantsar da Dr. Aliyu Isa Aliyu a matsayin Kwamishina a sabuwar ma’aikatar bunkasa al’amuran kiwon dabbobi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma rantsar da Barr. Salisu Muhammad Tahir a matsayin babban sakatare a ma’aikatar Sharia ta jihar Kano.
Da yake rantsar da sabbin kwamishinonin a yayin zaman majalisar zartaswa karo na 32, gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira garesu dasu zamo masu gaskiya da rikon amana a yayin gudanar da ayyukansu.
Ya ce nadin nadin nasu an yi shi ne bisa cancanta la’akari da gogewa da kwarewarsu da kuma irin gudummawar da suke bawa al’umar jihar Kano ta fannoni daban-daban.
Ya taya sabbin kwamishinonin murna tare da fatan zasu bada gudummawa wajen bunkasa cigaban jihar Kano.