Na yi lafiyayyen barci bayan soke faretin ranar yancin kan Nigeria – Tinubu

Date:

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce soke faretin zagayowar ranar ’yancin kai karo na 65 da sojoji ke yi ya ba shi damar yin lafiyayyen barci da kuma yin kyakkyawan kari a ranar Laraba.

Aminiya ta rawaito cewa Gwamnatin Tarayya ta soke bikin da aka shirya domin murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, daya ga watan Oktoba.

Sanarwar ta fito ne daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin.

Shugaban ya ce ya yi yamma mai daɗi a wajen ƙaddamar da cibiyar da Babban Bankin Najeriya (CBN) tare da haɗin gwiwar Bankers’ Committee suka ɗauki nauyin gyaranta.

Ya ce taron ya sauya abin da ya kira da salo ɗaya na faretin sojoji da ake yi a ranar ‘yancin kai.

Shin da Gaske Rikicin Masarautar Kano Ne Ya Hana Majalisar Dokoki Komawa Aikinta ?

“Gwamnatin Tarayya na sanar da soke bikin zagayowar ranar ‘yancin kai da aka shirya domin murnar cikar ƙasar shekara 65 a ranar Laraba, 1 ga Oktoba. Sokewar ba ta rage muhimmancin wannan rana ba,” in ji sanarwar da Daraktan Labarai da Hulɗa da Jama’a, Segun Imohiosen, ya sa wa hannu.

Da yake jawabi a ranar Laraba yayin ƙaddamar da cibiyar Wole Soyinka da aka gyara, wadda a da ake kira National Arts Theatre a Legas, Tinubu ya ce ya yi lafiyayyen barci bayan soke bikin.

“Barka da zagayowar ranar ‘yancin kai karo na 65. Wannan ya sauya salon maimaita faretin sojoji da duk abin da ke tattare da shi. Da aka soke wannan shiri, na samu yin lafiyayyen barci, na yi kyakkyawan kari, sannan na jira wannan yamma. Kuma yammar ta yi kyau,” in ji shi ga mahalarta taron.

Tinubu ya isa wajen taron da misalin ƙarfe 6:24 na yamma domin bikin buɗe wurin tarihin da aka gyara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Tinubu ya ba da Umarnin rage kudin aikin Hajjin 2026

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumar kula...

Hukumar yaƙi da cin-hanci ta jihar Kano ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da Naira biliyan 4 a Kano

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da...

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics ta Yi Allah-wadai da Yunkurin Siyasantar da Bikin Cikar Najeriya Shekara 65 a Kano

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics (FPA) ta yi Allah-wadai...

Yan Uwa da Abokan Arzikin Sabon Kwamishinan Shari’a na Kano Sun Shirya masa addu’o’i na musamman

Yan uwa da abokan arziki na kwamishinan shari'a na...