Shin gaske ne an dakatar da Mal. Lawal Triumph daga yin wa’azi?

Date:

Majalisar Shura ta Kano ta gayyaci malamin nan da ake zargi da furta kalaman “ɓatanci” ga janibin annabi Muhammad SAW a birnin Kano, Sheikh Lawal Triumph da ya je gabanta domin kare kansa.

Sakataren Majalisar Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya yi da yamamcin ranar Larabar nan a birnin na Kano.

Shehu Wada Sagagi ya kuma ƙara da cewa Majalisar ta dakatar da malamin daga tattauna batun da ake zarginsa da shi wanda ya janyo cece-kuce har zuwa lokacin kammala bincike bayan karɓar bahasinsa.

“Ba wai shi kaɗai Majalisar ta dakatar daga tattauna batun da ya janyo ruɗani har ma da dukkannin sauran malamai da al’ummar gari. Muna kira da a kame daga tattauna batun a jira har sai sakamakon binciken ya fito.” In ji Sagagi

Gaske ne an dakatar da Lawal Triumph daga wa’azi?

Sakataren majalisar ta Shura, Shehu Sagagi ya ce ba wai an dakatar da Lawal triumph daga yin wa’azi ba ne kwata-kwata.

“E an kawo shawara ne cewa wasu mutane suna ta fitintunu ana ta maganganu marasa daɗi har daga wajen jihar da ake ganin wannan abun zai iya hargitsa gari saboda haka aka kawo shawarar cewa a dakatar da shi daga dukkan waɗannan maganganu da suka shafi wannan mas’ala.”

Dangane da yadda Majalisar ta Shura ta tafiyar da al’amarin Shehu Wada ya ƙara da cewa:

Majalisar Shura ta zauna ta karɓi rahoto ƙarƙashin shugabancin Malam Mai Bushura a matsayin shugaba inda kuma Farfesa Babangida ya kasance sakatare.

“Sun karanta karatuttukan suka tsefe su, inda suka tantance da’awowin da masu ƙorafi ba su kawo wata hujja ba suka kuma ajiye su. Sannan kuma sun tantance waɗanda kuma suka bayar da hujja.”

“Sun kalli bidiyo kilif din da masu da’awa suka kawo. Kuma kwamitin nan ya yi adalci tunda sun faɗa cewa ko tari ya yi kan kowace mas’ala sun rubuta ta. An zauna an yi mahawara da nazari inda kwamitin ya bayar da shawarar da gayyaci waɗanda suka yi da’awa sannan kuma a kira shi wanda aka yi da’awa a kansa har ma da waɗanda suke sukar da’awar a kansa.”

“Daga baya gida ya amince cewa waɗanda suka yi da’awa babu hujja to a ajiye ta a gefe. Amma an ɗauki ƙorafin duk wata da’awa da aka yi da hujja. Hakan ya sa aka kafa kwamitin da ya gayyaci Malam Lawal domin baje masa abubuwan da ake zargin sa da su domin kare kansa.” Kamar yadda Shehu Wada Sagagi ya yi ƙarin haske.

Yadda za a yi zama da Malam Lawal Triumph

Shehu Wada Sagagi ya ce da farko za a fara da aike masa takardar gayyata tukunna wadda kuma za ta ƙunshi rana da lokacin da zai bayyana a gaban kwamitin.

Ya kuma ƙara da cewa domin cire shakku daga zukatan al’umma an shirya yin zaman kai tsaye.

“Wannan zama an shirya yin sa ne “Live” wato kai tsaye domin kowa ya ga irin tambayoyin da za a yi masa da kuma irin amsoshin da zai bayar,” in ji Shehu Sagagi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Tinubu ya ba da Umarnin rage kudin aikin Hajjin 2026

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumar kula...

Hukumar yaƙi da cin-hanci ta jihar Kano ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da Naira biliyan 4 a Kano

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da...

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics ta Yi Allah-wadai da Yunkurin Siyasantar da Bikin Cikar Najeriya Shekara 65 a Kano

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics (FPA) ta yi Allah-wadai...

Yan Uwa da Abokan Arzikin Sabon Kwamishinan Shari’a na Kano Sun Shirya masa addu’o’i na musamman

Yan uwa da abokan arziki na kwamishinan shari'a na...