Neman Mafita: Wani matashi da ya kammala Digiri ya koma soya wainar fulawa a Kano

Date:

 

Hausawa dai sun ce “Sana’a sa’a rashin sana’a sata”. Sannan Hausawa sun ƙara cewa “Sana’a maganin zaman banza”. A kwai kuma karin maganar da Bahaushe kan ce “Girman kai rawanin tsiya”.

Wani matashi mai suna Abubakar Umar Usman, ɗan unguwar Chiranci, Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano, ya dogara ne da sana’ar soye-soye domin ya tsira da mutuncin sa.

Shi dai Usman, wanda ya kammala digirin sa a fannin kemistri a Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano, a shekarar 2017, ya ce ya yanke hukuncin tsayawa da ƙafarsa ne domin ya daɗe ya na neman aikin gwamnati amma bai samu ba.

 

Bayan da ya kammala shirin bautar ƙasa, wanda a ka fi sani da NYSC, Usman ya nemi aiki a ma’aikatu da dama a faɗin ƙasar nan amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.

“Sana’a maganin zaman banza” in ji Hausawa, hakan ne ya sanya Usman ya yi tunanin ya fara sana’ar sayar da wainar fulawa domin ya riƙa samun kuɗin shiga don ya turawa kansa asiri.

“Kamar wasa, sai na yi tunanin na fara soya wainar fulawa ina sayarwa. Sai kusa na fara. Ban yi tunanin ni mai digiri bane, kawai na fara soya wainar fulawa a kofar gidan mu.

“Kamar wasa, sai na fara jan hankalin kwastomomi. Ƴan mata da matan aure, kai har ma da masu aure da angwaye suna zuwa su siya kullum. Har ta kai ta kawo ma wasu masu auren sun mayar da gurin da nake suyar gurin hirar su,” in ji Usman.

Daily Nigerian ta rawaito Usman ya ƙara da cewa da ya ga kasuwar ta sa kullum haɓaka ta ke, sai ya kama wani shago, inda ya ci gaba da sayar da wainar fulawa, sai ma ya haɗa da wainar shinkafa da miya, indomi, awara, shinkafa da sauran su.

A hirar da ya yi da wakilin Daily Nigerian Hausa, Usman, wanda ya buɗe wajen sayar da abinci mai suna AU Square, ya ce kwata-kwata ba ya jin kunyar sayar da abincin, in da ya ƙara da cewa “suma ƴan matan burge su na ke yi.”

Usman ya ce yana da ma’aikata da su ke aiki a ƙarƙashin sa, har ma da waɗanda ya ke biya naira dubu 12 a wata a kusan shekara uku kacal da fara sana’ar.

Ya ƙara da cewa shi yanzu abinda ya ke samu a sana’ar ta sa ko aikin gwamnatin ya samu, ba kowanne ne zai samu kuɗin kamar yadda ya ke samu a sayar da abinci ba.

“Ni fa ma’aikatan gwamnati da ma na Ma’aikatu masu zaman kan su ba kowane zai fini samu ba. Gaskiya dai rayuwa alhamdulillah, asiri ya rufu. Ni ba na ma tunanin sake neman aiki a halin yanzu,”

Usman ya ƙara da cewa shi burin sa ya sake bunƙasa sana’ar sa ya zamana ya bada gudunmawar sa ga tattalin arziƙin Jihar Kano da ƙasa baƙi ɗaya.

3 COMMENTS

  1. Toh
    MALLAM Usman Allahu ya dafa maka Allahu ya taimaka mana haka mukeson jaruman maza, Allahu yabamu da mutuwar zuciya

  2. קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. מכוני ליווי

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...