Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin jagorancin Mai Shari’a Josephine Obanor, ta tabbatar da cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) na da cikakken ikon gudanar da bincike kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗen tallafin karatu na jihar Kano.
Majiyar Kadaura24 ta Solacebase ta ce Rahoton ya bayyana cewa, ICPC ta gayyaci jami’an Ma’aikatar Ilimi mai zurfi ta jihar Kano dana hukumar tallafin karatu domin su kawo wasu takardu da kuma bayyana wasu bayanai da ake bincike a kansu.
Sai dai, babban sakataren ma’aikatar, Dr. Hadi Bala, tare da wasu jami’an, sun shigar da ƙara a kotu suna masu neman kotun ta hana binciken domin yin binciken ko gayyyararsu tauye musu ’yancin su ne na dan Adam.
Da fari dai ita hukumar ICPC korafi ta samu game da zargin wata almundahana da aka ce an yi a hukumar lamarin da ya sanya ta fara bincike, Wanda hakan yasa aka kata kara Kotu.
Yayin yanke hukuncin Kotun ta yi watsi da wannan ƙara, inda ta bayyana cewa:
1. Gayyatar ICPC ba take hakkin kowa ba – Domin kawai neman takardu ko bayanai don bincike ba ya nufin tauye ’yancin ɗan adam.
2. Kotun ta ce shigar da Babban lauyan Kasa shi cikin ƙarar bai da amfani.
3. Kotun ta jaddada cewa hukumar ICPC tana da ikon gudanar da cikakken bincike kan duk wani zargin almundahana da kudaden gwamnati.

Wannan hukunci ya sake tabbatar da cewa babu wanda ya fi karfin doka, kuma an bai wa ICPC ƙarfin iko wajen tabbatar da gaskiya da ingantaccen amfani da kuɗaɗen jama’a, musamman kuɗin da aka ware domin tallafawa ɗalibai.