Vice-Admiral Ibok-Ete Ibas (Mai ritaya), wanda shi ne gwamnan riko na soji na Jihar Rivers, ya ce ya cika aikin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi.
Da ya ke magana a gidan gwamnatin jiha a Port Harcourt, yayin gabatar da rahoton zaben kananan hukumomi da hukumar zabe ta jihar Rivers (RSIEC) ta gudanar.
Ibas ya ce umarnin da shugaban ƙasa ya ba shi shi ne ya dawo da jihar zuwa cikakken mulkin dimokuraɗiyya da zaman lafiya.
Ibas ya ƙara da cewa, da gudanar da zaɓen kananan hukumomi da kuma rantsar da shugabanninsu, “an cimma burin nauyin da aka ɗora a wuya na.”