A ranar Litinin 8 ga watan Satumbar 2025, ne kungiyar ƙwadago ta ma’aikatan dakon man fetur da iskar gas a Najeriya, NUPENG, za ta shiga yajin aiki domin adawa da matakin da matatar mai ta Ɗangote ta dauka na fara kai man fetur zuwa gidajen mai da ke fadin ƙasar.
Ƙungiyar ta NUPENG, ta zargi matatar Dangote da karya dokokin ƙwadago inda ta ce yana neman raba direbobin da ke dakon mai da aikinsu.
Kungiyar ta NUPENG, ta ce muddin matatar mai ta Dangote ta fara jigilar mai zuwa gidajen man da ke jihohi, to dubban ma’aikatan da ke aiki a depo-depo da kuma direbobin da ke tuka manyan motoci sama da dubu 30, za su rasa aikinsu.
Kwamared Lawan Garba, shi ne mataimakin shugaban kungiyar direbobin tankar mai ta PTD, daya daga cikin kungiyoyin kwadago da ke NUPENG, ya shaida wa BBC cewa, a doka babu wani mai kamfani kamar na Dangote, wanda ke depo da gidan mai sannan a sayi kaya ya kuma dauka ya kai, sam doka bata bayar da wannan dam aba.
Ya ce,” Dalili shi n esu masu dakon mai idan hakan ta kasance za su zamanto basu da aikin yi ke nan, sannan mutanen da za su rasa aiki suna da dama tun da akalla yanzu muna da tankuna sama da dubu 30 da ke zirga-zirga, to idan aka ce a yau tankuna sun tsaya to ai masu tuka su ma aiki ya tsaya musu.”
Za mu yi Aiki ba Dare ba Rana domin Tabbatar da Umarnin da Ganduje ya ba mu -Baffa Babba Danagundi
Kwamared Lawan Garba, ya ce: ” A don haka idan har matatar mai ta Dangote ta fara aiki da wannan mataki, to ko shakka babu muma zamu dauki matakin fara yajin aiki.”
Ita ma kungiyar masu gidajen mai da isakar gasa NUGASA, ta nuna goyon bayanta a kan matakin da NUPENG din ta ce zata dauka na shiga yajin aiki.
Abdullahi Idris, shi ne mataimakin shugaban kungiyar NUGASA a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa su ma basu yar da da wannan tsari na Dangote ba, saboda muna tare da NUPENG.
Ya ce,” Idan har Dangote zai rika kai mai gidajen mai da motocinsa, to mu me zamu yi ke nan? Ta karfi an fitar da mu a cikin sana’ar da muka dade muna bauta a kanta.”
A bangare guda, kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya IPMAN, kira ta yi ga dukkan bangarorin biyu da su kai zuciya nessa.

Alhaji Abubakar Mai Gamji Shettima, shi ne shugaban IPMAN a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa su son kungiyar NUPENG da PTD da NARTO, da su kai zuciya nessa.
Ya ce,” Ya kamata wadannan kungiyoyi su zauna da Dangote domin a sasanta domin mu ba ma son duk wani abu da zai jefa talaka cikin wahala, don haka yanzu su zo mu hada kai da Dangote a warware wannan matsala.”
Tuni dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi kira ga kungiyar NUPENG da ta dakatar da shiga yajin aikin da ta ke shirin farawa.
BBC Hausa