Babban Darakta na Hukumar NPC na kasa Dr. Baffa Babba Dan Agundi ya bayar da tabbacin cewa za su yi aiki ba dare ba rana domain tabbatUar da umarnin da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ba su.
Baffa Babba ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da kwamintin mutum 44 wadanda za su tantance ‘yan Hisba Mutum 1,000 da Gwamnatin Kano mai ci ta kora daga aiki.
Babba dan Agundi ya bukacin yan kwamitin dasu tabbatar tareda tantance duk wadanda suka san Dan Hisba ne wanda Gwamnatin jihar Kano ta kora daga aiki domin nema masa mafita kamar yadda tsohon Gwamnan Kano Kuma tsohon shugaban Jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya umarce su.