Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta aike da takardar gayyata ga shugaban Karamar Hukumar Dala da kuma shugaban Makarantar Koyon Aikin Shari’a ta Aminu Kano (Legal) bayan gano rashin samunsu a wurin aiki.
Shugaban hukumar, Comrade Sa’idu Yahaya, ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar bazata da ya kai a wasu muhimman ma’aikatun gwamnati da suka haɗa da Asibitin Murtala Muhammad, Sakatariyar Karamar Hukumar Dala, da kuma Makarantar Legal.
Ya ce hukumar ba za ta lamunci sakaci ko kin bin doka daga ma’aikata ba, inda ya gargadi cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci ladabtarwa.
Comrade Sa’idu ya koka da ƙarancin manyan ma’aikata a sakatariyar Dala da makarantar Legal, yana mai cewa irin wannan rashin zuwan aiki na iya kawo cikas ga ci gaban da gwamnati ke ƙoƙarin kawowa.

Sai dai ya yaba da ƙoƙarin ma’aikatan Asibitin Murtala, musamman a sashen haihuwa da na agajin gaggawa, inda ya ce sun gamsu da yadda suka same su tsaye bakin aiki.
“Za mu ci gaba da ladabtar da masu sakaci yayin aiki, sannan kuma za mu karrama waɗanda muka samu suna gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Wannan zai ƙara musu ƙwarin gwiwa da sha’awar aiki,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ziyarar bazata na cikin sabbin matakan hukumar wajen sanya ido kan yadda ake gudanar da ayyukan gwamnati a dukkan matakai.