Rundunar Yan Sanda Ta Kano Ta Bayyana Nasarorin Da Ta Samu a Shirin Operation Kukan Kura

Date:

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa rundunar ta samu gagarumar nasara wajen yaki da aikata laifuka a watan Agusta, sakamakon sabbin dabarun da ake amfani da su a karkashin shirin “Operation Kukan Kura”.

A taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar ’yan sanda ta Bompai, Kano, ranar Litinin, Bakori ya ce rundunar ta samu nasarar cafke mutane 107 da ake zargi da aikata manyan laifuka, ciki har da fashi da makami, safarar miyagun kwayoyi, satar mota da babura, da kuma tada tarzomar ’yan daba.

FB IMG 1753738820016
Talla

Masu laifin da aka kama sun hada da:
Yan fashi da makami: 8
Masu garkuwa da mutane: 8
Masu safarar mutane: 3
Masu safarar miyagun kwayoyi: 14
Masu satar mota: 2
Masu satar babura: 6
Masu sata daban-daban: 5
’Yan daba: 61.

Kwalejin Sa’adatu Rimi Ta Nemi Gwamnati Ta Mayar Da Hankali Wajen Fassara Litattafan Ilimin Zuwa Hausa

Abubuwan da aka kwato sun hada da:

Bindiga AK-47 guda 1 da bindigogi na gida 7, da harsashi 11, sai Motoci 7, babura 8, da shanu 7 da Adduna 102, wukake 74
Ganyen wiwi da ake zargi ta kai 111 parcels da 458 wraps Magungunan da ake amfani da su wajen sa maye.

Akwai kuma Tufafin kampala guda 44, da wayoyin salula 59, na’urar POS 3, katunan Opay 17, da sauran kayayyaki.

Kwamishinan ya kara da cewa tun lokacin da aka kaddamar da “Operation Kukan Kura” a ranar 1 ga Yuli, an kwato makamai masu hatsari har guda 473 da kuma tarin miyagun kwayoyi.

Ya ce manufar shirin ita ce hada kai da al’umma wajen yaki da aikata laifuka, inda jama’a ke taka muhimmiyar rawa a matsayin idanu da kunnuwan rundunar ’yan sanda a unguwanninsu.

Kwamishinan ya yaba wa jami’ansa bisa sadaukarwar da suke yi da kuma jama’ar Kano bisa hadin kai da goyon baya, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani abu da ake zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...