Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada, Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u (Soja), ta gudanar da rabon kayayyakin arziki ga mazauna karamar hukumar da kuma magoya bayan jam’iyyar NNPP Kwankwasiya
Wannan taron rabon tallafin ya kasance mai armashi, inda aka raba kayayyakin da suka shafi fannoni daban-daban na rayuwa, musamman na kiwon lafiya, ilimi, sufuri, da sana’o’in dogaro da kai. Kayayyakin da aka raba sun haɗa da:
Shugabar ta raba Keken guragu guda 50 Domin tallafa wa masu bukata ta musamman.

Ma’aikatan lafiya 120 An ɗauke su aiki tare da basu takardun kama aiki domin ƙara inganta fannin lafiya a yankin.
Baburan hawa guda 60 domin tallafa wa matasa da ‘yan kasuwa su samu ababen hawa don sana’o’i.
Kekunan hawa guda 50 an bayar dasu ne ga jamia’a da kuma dalibai don su samu damar zuwa makaranta cikin sauƙi.
Keken dinki 100 domin baiwa mata da matasa masu sana’ar dinki damar haɓaka sana’o’insu.
Wayoyin hannu 30 ga matasan social media domin ƙarfafa masu yada manufofin gwamnati da jam’iyyar NNPP
Kudaden jari ga matasa da mata domin su cigaban sana’oinsu.
Hajiya Sa’adatu ta bayyana cewa wannan rabon tallafi na daga cikin shirye-shiryen jam’iyyar NNPP da jagororin ta wajen ciyar da al’umma gaba. Ta jaddada cewa wannan aikin yana gudana ne da goyon bayan Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon Gwamna, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, da Mai dakinta jagora jigo a jam’iyyar NNPP, air Comando Yusha’u Salisu (Soja).
Ta kuma tabbatar da cewa zataci gaba da kawo shirye-shirye da zasu amfanar da al’umma, musamman talakawa, matasa da dalibai – inda ta bada tabbacin ci gaba da raba kekunan hawa ga daliban makaranta domin sauƙaƙe musu hanyoyin zuwa makaranta.
Al’umma daga sassa daban-daban na Karamar Hukumar Tudun Wada sun nuna farin ciki da godiya ga wannan gagarumin tallafi, tare da sake jaddada goyon bayansu ga Hajiya Sa’adatu da jam’iyyar NNPP.