Ana sa ran Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai isa Legas babban birnin kasuwanci na Najeriya domin ƙaddamar da wasu ayyuka a yau.
Rahotanni na cewa cikin ayyukan da zai ƙaddamar har da wasu sabbin jiragen ruwa na yaƙi a sansanin sojin ruwa da ke Victoria Island.
Tuni hukumar kiyaye haɗura ta jihar Legas LASTMA ta ba jama’a shawara da su kiyayi bi ta titin Ahmadu Bello sakamakon ziyarar shugaban.
BBC Hausa ta rawaito tuni sojoji da ƴan sanda da jami’an DSS 1suka cika unguwar Victoria Island wanda nan ne shugaban zai je.
Ana kuma sa ran bayan ƙaddamar da ayyukan zai halarci ƙaddamar da wani littafi wanda Chief Bisi Akande ya rubuta.