Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Hon. Anas Mukhtar Bello Danmaliki, ya nada Farfesa Mamunu Mustapha a matsayin sabon Sakataren Ilimi na karamar hukumar .
Wannan mataki dai na daga cikin shirye-shiryen da ake yi don inganta harkar ilimi a karamar hukumar, inda ake sa ran kwarewa da gogewarsa za su taimaka wajen magance matsalolin da ke addabar dalibai da malamai.

Farfesa Mamunu Mustapha malami ne da yake koyar da Injiniyan Wutar Lantarki a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, inda ya shafe sama da shekaru 20 yana aiki a fannin jagoranci da tsara manufofin ilimi. Ya rike mukamai da dama a wannan jami’ar.
A bangaren dalibai kuwa, Farfesa Mustapha ya taba shugabantar Kungiyar Daliban Dawakin Tofa, kuma a yanzu shi ne Shugaban kungiyar DAF, wacce ta kunshi malaman jami’o’i na karamar hukumar Dawakin Tofa. Kungiyar na gudanar da ayyuka na tallafa wa dalibai da bunkasa binciken kimiyya.
Yayin bikin Mika mashi takardar kama aiki, Shugaban karamar hukumar Anas Mukhtar Bello Danmaliki ya bayyana cewa suna da yakinin Farfesa Mustapha zai kawo sauyi a fannin ilimi.
“Muna farin cikin samar da ku cewa Farfesa Mamuni zai yi amfani da Kwarewarsa da jajircewarsa wajen ganin dalibai sun sami ci gaba, wanda hakan ne ya sa muka zabe shi. Mun yi imanin karkashinsa za mu ga gagarumin ci gaba a makarantunmu.” Inji Danmaliki
Gwamnatin Kano ta kafa Kwamitin don bincikar Ganduje kan zargin sayar da mayanka
Shi ma a nasa jawabin, Farfesa Mustapha ya yi alkawarin hada kai da malamai, iyaye da shugabannin al’umma don tabbatar da kowane yaro ya samu ingantaccen ilimi.
“Wannan dama ce babba, kuma zan yi amfani da ita wajen kawo sabbin hanyoyin warware matsalolin makarantunmu tare da al’umma gaba ɗaya.”
Karamar Hukumar Dawakin Tofa dai ta sha daukar matakai na inganta ilimi, ciki har da gyaran makarantu, samar da kayan koyarwa da horar da malamai. Ana sa ran sabon sakataren zai kara karfafa wadannan shirye-shirye.