Lauyan jam’iyyar NNPP, Barista Ndubuisi Ukpai, ya rubutawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) wasika, inda ya bukaci hukumar ta dakatar da duk wani zabe har sai an tabbatar da sahihin tambarin jam’iyyar a takardun zabe.
Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da jam’iyyar ta rabawa manema labarai a ranar Laraba a Legas.

A cikin wasikar, lauyan ya bayyana cewa bai kamata INEC ta gudanar da wani zabe ba har sai ta saka sahihin tambarin NNPP, tare da amincewa da jagorancin Dr. Major Agbo a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.
“Mu ne lauyoyin da ke wakiltar sahihin shugabancin NNPP karkashin jagorancin Dr. Major Agbo, don haka muka rubuto wannan wasika bisa umarninsu.
“Muna gargadi da cewa bai kamata INEC ta halarta, ta sa ido, ko kuma ta nuna wata alaka da wani bangare ba . Yin hakan zai zama tsoma baki kai tsaye a cikin shari’ar da ke gaban kotu, kuma abin kunya ne ga dokokin kasar.
NLC ta yaba wa Gwamna Kaduna bisa dawo da malaman makaranta da El-Rufai ya kora
“Mun fitar da wannan wasika domin tunatar da hukumar cewa ya kamata ta dawo hayyacinta ta hanya bin doka da yin abun da ya dace .
“Muna fatan INEC za ta yi aiki cikin kwarewa da bin ka’idojin doka kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada,” in ji wasikar.