Kungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC), reshen Jihar Kaduna, ta yaba wa Gwamna Uba Sani bisa dawo da wasu daga cikin malaman makaranta da gwamnatin Nasir.El-Rufa’i ta kora a jihar.
Shugaban NLC na Jihar Kaduna, Ayuba Suleiman ne ya yi wannan yabo yayin da ya ke jawabi ga mambobin Kungiyar ‘Yan Jaridu Masu Bincike ta Ƙasa (NGIJ) wadanda ke jihar domin duba yadda ake tafiyar da mulki.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito gwamnatin da ta gabata Kaduna karkashin Nasir El-Rufai ta kori malamai sama da dubu 23, ciki har da tsohon Shugaban Kungiyar Malaman Makaranta ta Kasa (NUT), tsakanin shekarar 2018 zuwa 2021.
Wani Gwamna a Nigeria ya ƙara mafi ƙarancin albashi daga N76,000 zuwa N104,000
Suleiman ya bayyana cewa gwamnatin Kaduna mai ci ta dawo da shugabannin makarantu, ma’aikatan gudanarwa da malamai na koyar da kimiyya da abin ya shafa, yana mai cewa ana ci gaba da gyara kura-kuran da gwamnatin baya ta tafka.