Gwamnan Kano ya magantu kan zargin karkatar da Naira Biliyan 6.5 da ake yiwa hadiminsa

Date:

Gwamnatin Kano ta musanta zargin da ake yi wa hadimin gwamnan Kan harkokin tafiye-tafiye da karbar baki Abdullahi Rogo na karkatar da kudin da yawansu ya Kai Naira Biliyan 6.5 .

Cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnatin Kano ta ce kafafen yada labarai na zamani a cikin ‘yan kwanakin nan sun cika da labaran karya da suka danganci batun rikon amana da kuma ikon ta’ammali da kudi na wasu manyan mukarraban gwamnatin Jihar Kano a harkokin siyasa.

Da dumi-dumi: Sanarwa ta Musamman daga Gwamnatin jihar Kano

Daya daga cikin labaran wanda aka yi la’akari da shi, shi ne wanda jaridar Daily Nigerian, kafar yada labarai ta yanar gizo ta wallafa, a ranar 22 ga watan Agusta, 2025, wanda ya ja hankalin gwamnati musamman kan zargin cirewa da karkatar da naira biliyan 6.5 daga baitul malin gwamnati.

Babban abin da ya shafi almubazzaranci da dukiyar jama’a, wanda tuni aka shigar da kara a gaban babbar kotu, shi ne babban daraktan kula da harkokin jama’a na gidan gwamnatin jihar Kano, Alh. Abdullahi Rogo.

FB IMG 1753738820016
Talla

Sanarwar tace ba tare da la’akari da shari’ar da ake ci gaba da yi a kan lamarin ba, ya zama wajibi gwamnatin jiha ta baiwa al’umma bayanai na ayyukan Hukumar Kula da Jama’a a gidan gwamnatin Kano, wanda bai banbanta da tsarin da ake samu a dukkan jihohi da gwamnatin tarayya ba.

Gwamnatin tace Hukumar da ke kula da ka’idojin gwamnati da jama’a karkashin Malam Rogo, tana gudanar da muhimman ayyuka a gidan gwamnati da kuma muhimman ayyuka a ofishin gwamna.

Wadannan ayyuka sun shafi kayan aiki, masauki, jin dadi, da kula da zirga-zirgar Gwamna a ciki da wajen kasar nan.

Haka nan an bai wa ofishin damar samar da kayan aikin da ake buƙata ga manyan baki waɗanda suka haɗa da Fadar Shugaban ƙasa, Ministoci, mataimakan ƙasashen waje, da sauran baƙi na diflomasiyya a ziyarar aiki ga Gwamna.

Zargin Almundahana: EFCC da ICPC Sun Gano Naira Biliyan 6.5 A Asusun Guda Cikin Manyan Hadiman Gwamnan Kano

Sanawar tace sama da kashi 95 cikin 100 na nauyin da ya rataya a wuyan hukumar ya shafi hada-hadar kudi da yawa kuma a mafi yawan lokuta, suna warware bashin da ake bin jihar ta fuskar gudanarwar yau da gobe.

Sanarwar ta kara da cewa a yayin da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da mai da hankali kan harkokin mulki tare da kiyaye matsayinta na bin doka da oda, da bin diddigin gaskiya, da rashin kawar da kai ga cin hanci da rashawa, gwamnati ba za ta sadaukar da mutuncin mataimakanta ba wajen aiwatar da ayyukan bata-gari na siyasa da wasu marasa kishin kasa ke shiryawa.

Daga ƙarshe,Gwamnatin ta ce ba ta kokwanton sahihancin Darakta Janar na Kula da Jama’a na Gidan Gwamnati, Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...