Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce nan ba da jimawa ba za a bayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci a ƙasar tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
Ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels , inda ya ce jinkirin ya samo asali ne daga rikice-rikicen shari’a da kuma alakar wasu daga cikin kuɗaɗen da ake amfani da su wajen daukar nauyin ta’addanci da ƙasashen waje.

Musa ya ce an gano wasu daga cikin masu daukar nauyin suna cikin ƙasar, inda sukan ɗauki matasa aiki, su ba su babura, sannan su rika tura kuɗaɗe zuwa wasu asusun ajiya a kullum.
Ya yabawa Hukumar NFIU bisa rawar da take takawa wajen gano kuɗaɗen ta’addanci, tare da bayyana cewa Ma’aikatar Shari’a, ofishin Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa da sauran hukumomi suna aiki don tabbatar da an hukunta masu hannu a lamarin.
Wasu yan daba sun ajiye Makamansu a Kano
Ya kuma ce hukumomin tsaro suna bin diddigin wasu ‘yan siyasa da ake zargi suna tallafawa rashin tsaro domin amfanin kansu.
Najeriya na ci gaba da fama da matsalar ta’addanci musamman a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, inda Boko Haram da ‘yan bindiga ke addabar jama’a.