Wasu yan daba sun ajiye Makamansu a Kano

Date:

Gwamnatin Jihar Kano Hadin gwaiwa da Rundunar Yansandan Jihar kano ta kaddamar da tantance Tubabbun Yan Daba 75 Kashi na farko cikin 1,500 da suka Ajiye makaman su ta cikin Shirin tudun mun tsira wato safe corridor project.

Dayake jawabi a Wurin Taron Wanda ya gudana a shelikwatar Rundunar Yan Sanda dake Bampai, Gwamnan Jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf Wanda ya samu wakilcin Kwamishinan yada labarai da Ayyukan cikin gida kwamarade Ibrahim Abdullahi Waiya yace, tantacewar Rundunar Yansandan ita ce ta farko nan gaba kuma Hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA zata Kara tantance matasan.

FB IMG 1753738820016
Talla

Daga nan gwamnatin Jihar kano zata cika Alkawarin data dauka na bada jari ga tubabbun matasan masu sha’awar kasuwanci da kuma Samar da gurbin karatu ga masu sha’awar komawa makaranta.

A jawabin sa sarkin kano Mal. Muhammadu Sunusi na II Wanda sarkin shanun Kano Alh. Muhd Shehu ya wakilta ya taya matasan murna, Wanda ya bukaci su Zama jakadu Wurin yaki da Daba da kwace a Jihar nan.

Masu Mukamai a gwamnatin Kano ba su da uzurin kin taimakawa yan Kwankwasiyya – Sanusi Bature

Babban kwamandan Hisba Mal. Aminu Ibrahim Daurawa na daga cikin kwamitin Lura da tabbatuwar Shirin yayi Nasiha ga matasan cewa su Tabbatar sunyi tuban da ba zasu Kara komawa wajen aikata barna ba.

Ya kuma godewa Gwamnatin Kano tare da bawa matasan shawarar cewa suja hankalin yanuwansu Wurin yadda makamansu don Suma su Amfana da Shirin.

Taron ya samu halartar Iyaye, Babban Kwamandan bijilanti Shehu Rabi’u,Kwamandan NDLEA na Kano Abubakar Sadiq Ahmad
Dan Amar Hakimin gobirawa wakilin kwamitin Zaman lafiya da sauran Shugabannin Kungiyoyi da masu ruwa da tsaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...